Posts

Showing posts from April, 2019

An haifi jaririya mai kai biyu a Sokoto

Image
Jariri mai kai biyu An haifi jaririyar mai kai biyu a asibitin General Hospital wanda ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato. Mahifiyar jinjirar ta isa asibitin ne da misalin karfe biyar a ranar Alhamis din da ta gabata bayan da ta shafe sa'o'i tana nakuda a gida, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Wata jami'an asibitin ta gano cewa matar ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda jinjirar ta zo da kaffafu maimakon da kai, sai ta bukaci taimakon likitoci a asibitin. Likitocin ne suka gudanar da bincike kan matar kuma suka gano cewa jaririyar ta riga ta mutu saboda dadewar da matar ta yi tana nakuda kafin ta je asibitin. Daya daga cikin likitocin da suka duba matar, Dokta Malami Muhammad Gada ya ce sun fuskanci matsaloli da dama wajen kokarin fida jinjirar saboda yadda kan ta yake da nauyi. ''Matar ba ta taba zuwa awon ciki ba lokacinda take da juna biyun, lamarin da ya janyo ba a iya gane yanayin jinjirar ba da wuri,'' in ji shi. Image ...

An kashe mutum 3,500 a Zamfara a shekara biyar

Image
Gwamna Abdul'aziz Yari An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wasu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammad shinkafi ya shaida wa BBC. Ya ce alkalunma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na kasar gona. Farfesan ya ce sun tantance hakan ne saboda duk lokacin da 'yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura tawaga a kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya. Har ila yau ya ce akwai mutane da dama da rikicin ya raba da muhallansu. Ya kuma ce rikicin ya fi shafar harkar noma. Ya ce suna ba jami'an tsaro dukkannin goyon bayan da ya dace wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar. A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya ta dakatar da aikace-aikacen hakar ma'adanai a jihar. Ko mene ne dalilin dakatarwar? Adamu ya ce an yi hakan ne "bisa la'akari da bayanan...

Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri

Image
Shugaba Muhammadu Buhari Mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana dalilin gwamnatin tarayya na dakatar da hakar ma'adinai a jihar Zamfara. Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu bayanan sirri kan alakar da ke tsakanin hare-haren da ake kai wa a yankin da kuma hakar ma'adinan da ake yi. Sai dai bai fito fili ya bayyana irin bayanan da gwamnatin ta samu ba game da alakar hakar ma'adinan da kuma barnar da ke faruwa a jihar ta Zamfara. Amma ya bayyana cewa matakin da aka dauka na da alaka da matsaloliin da jihar ke fuskanta. Ya ce ban da 'yan Najeriya, akwai wadanda ba 'yan kasa ba da dama da suke aikin hakar ma'adinai inda wasu ke yi bisa ka'ida wasu kuma ba su da lasisin yin hakan. Garba Shehu ya bayyana cewa ya kamata jama'a su yi hakuri domin gwamnati na nan na bincike kuma jama'a za su samu gamsuwa da sakamakon da gwamnati za ta fitar. Ya ce akwai hadakar rundunonin da aka kafa na sojojin kasa da na sama...

'Yan Najeriya ba su yi min adalci ba kan Zamfara- Buhari

Image
Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari ya bara kan kashe-kashen da ake fama da shi a jihar Zamfara, inda ya mayar da martani ga masu zangar-zangar Allah-wadai da al'amarin. Buhari ya ce kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya su ne abin da ya saka a gaba a kodayaushe, saboda haka rashin adalci ne a ce bai damu da abin da yake faruwa ba. Yana wannan batu ne daga yankin Gabas Ta Tsakiya, inda yake amsa gayyatar wasu sarakunan Larabawa don shiga taron tattalin arziki na duniya. "Shashanci ne da rashin adalci a ce ban damu da abin da yake faruwa ba a Jihar Zamfara ko kuma a ce ba na yin komai game da lamarin," Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter. Ya kara da cewa "kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya su ne abin da na saka a gaba a kodayaushe. Babu wani abu da ya sha gaban haka." Ya ci gaba da cewa: "A shirye muke don kawo karshen wadannan tambadaddun 'yan bindiga. Mun tura jami'an tsaro zuwa lungu da sako inda abin ke faruwa kum...

Zamfara: Manyan malamai sun ja-kunnen Buhari

Image
Shugaba Buhari Wasu manyan-manyan malaman addinin Musulunci sun yi kira da babbar murya ga Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da su kawo karshen kisan gillar da ake yi wa jama'a a sassa da dama na Najeriya. Ko a ranar Asabar an kashe mutane da dama a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna, ba ya ga gwamman da ake yi wa kisan gilla akai-akai a jihar Zamfara da wadanda ake sacewa domin neman kudin fansa, abin da ya sa 'yan kasar yin zanga-zanga a ciki da wajenta. Wannan ya sa malamai da dama yin huduba ta musamman a ranar Juma'ar da ta gabata domin yin Allah-wadai da abin da yake faruwa da kuma neman gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su dauki mataki. "Muna kira ga mahukunta da su tashi tsaye domin kare jama'a da samar musu da zaman lafiya domin hakkin mutane ne a kansu, kuma sai Allah Ya tambaye su," a cewar babban malamin nan na Kano, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo. "Duk wanda ke da [hakkin] ya yi wani abu, to sai Allah Ya tsare shi a ranar...