Posts

Showing posts from July, 2019

APC ta dakatar tare da neman a kori Abdulmumin Jibrin Kofa

Image
Abdulmuminu jibrin Jam'iyyar APC a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano ta kori dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, tare da neman uwar jam'iyyar ta kore shi gaba daya. A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bebeji, Suleiman Gwarmai, ya sanya wa hannu, ya ce an dakatar da dan majalisar mai wakiltar ne a mazabarsa, saboda yana yi wa jam'iyyar zagon-kasa. Alhaji Suleiman ya ce an dauki matakin ne bayan da wani kwamiti mai mutane bakwai da jam'iyyar ta kafa bayan da ta samu korafi a kan dan majalisar, ya yi bincike ya kuma mika rahotonsa. Kawo Abdulmumini Jibrin bai mayar da martani ba kan wannan sanarwa. BBC ta tuntube shi a waya amma bai amsa kiran ba. A baya-bayan nan dan majalisar ya samu kansa cikin rikicin siyasa tsakaninsa da wasu gaggan jam'iyyar a Kano. Kuma rahotanni sun ambato shi yana cewa yana shirin barin majalisa domin komawa jami'a saboda yana so ya zama farfesa. Y...

An 'kashe' dan Osama Bin Laden, dan gidan Osama

Image
Hamza bin laden Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce an kashe Hamza Bin Laden, dan tsohon shugaban kungiyar Al-ka'ida marigayi Osama Bin Laden. Har yanzu ma'aikatar tsaron Amurka ba ta bayar da wani karin haske kan mutuwar tasa ba. A 'yan watannin da suka gabata kasar ta sanya ladan dala miliyan daya kan duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Hamza Bin Laden, mai shekara 30. A lokacin sun ce yana kokarin zamowa wani babban kusa a shugabancin kungiyar ta Al-ka'ida. Sun kara da cewa ya yi amfani da sakonnin murya da bidiyo domin yin kira a kaiwa Amurka da kawayenta hari - domin ramuwar gayya ga kisan mahaifinsa. A shekarar 2011 ne dakarun Amurka suka kashe Osama Bin Laden - wanda aka zarga da taimakawa wurin shirya hare-haren 11 ga watan Satumba bayan shafe shekara 10 ana nemansa. An kuma gano wasu takardu a gidan da aka kashe shi a Pakistan, wanda aka ce shi ya rubuta, inda ya ce yana horas da dan nasa domin ya gaje shi.  R...

Tatattun bayanan Firar da akayi da Gwamnan Zamfara

Image
Gwamna Matawalle Yafara da yiwa al'ummar jihar Zamfara godiya akan wadannan nasarori da Gwamnatinsa ke samu ya bayyana wannan nasara dacewa addu,ar da Yan Zamfara suka Dade sunayi ce takawo wannan nasara. Yakuma bayyana sulhun da suka da Yan bindiga Sulhu ne fasukayi tsakani da Allah Babu yaudara aciki kuma za'a samu tabbataccen Zama lfy Mai dorewa a jihar Zamfara. Yakumace bayan zuwansa Kanoma ansamu matsaloli dasuka Kai har akadakatar da Sarkin Maru. Bayan wannan yaje yasamu Shugaban kasa Buhari yabashi bayanai akan yanda matsalar tsaro jihar Zamfara take, kuma Shugaban kasa yaji dadi da zuwansa yakuma yimasa alkawarin yimasa duk abinda yakeso Domin Zamfara ta zauna lafiya, sannan Shugaban kasa yabada taimakon buhun taki duhu dari da arba'in da takwas da dari biyar 148,500, kuma Shugaban kasa yabada dama ayi binciki aga irin barnar da akayi azamfara Domin aginama wasu da wannan matsala ta shafa gidaje. Yakumace Fita ta ta farko da yayi zuwa saudiyya don in go...

Duk mabiyin El- Zakzaky dan ta'adda ne - 'Yan sanda

Image
Ibrahim El-zazzaky Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce daga yanzu za su dauki duk wani dan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a a matsayin dan ta'adda bisa la'akari da hukuncin babbar kotu da gwamnati ta samu. Sifeto Janar wanda ya bayyana hakan a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja a yayin wani taron manyan 'yan sanda na wata-wata ranar Talata, ya ce ayyukan kungiyar da yunkurin jefa Najeriya rikicin kabilanci. Mohammed Adamu ya yi karin haske dangane da mambobin kungiyar IMN 63 da suka hada da mata bakwai wadanda ke hannun 'yan sandan, inda ya ce daga yanzu duk dan kungiyar ta IMN da suka kama to za su gurfanar da shi ne a gaban kotu domin fuskantar hukunci irin na ta'addanci. Ya kara da cewa " ayyukan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da Sheikh Zakzaky ke jagoranta sun dade suna barazana ga tsaro da doka da oda na Najeirya da kuma zaman lafiya da jogaranci na gari da ma kimar ta...

Banbancin Gwamnatin Matawalle data Audu Yari

Image
Gwamna Bello Matawalle Tun bayan rantsar dashi amatsayin Gwamnan jihar Zamfara Acikin sati daya da bashi mulki Gwamna Matawalle yaziyarci yankin Mada Wanda yakunshi Gurbin bore da Wonaka dake karamar hukumar mulkin Gusau, wannan yanki, yankine da yayi fama da hare, haren Yan bindiga da barayin shanu, Amma a tsohuwar Gwamnatin data gabata Babu wani jami'in tsohuwar Gwamnatin daya taba koda kaimusu ziyara koda da niyar yimusu jaje, Amma Bello Matawalle yataka da kafarshi yaje wannan yanki yakuma Basu alwashin za'a magance wannan matsala cikin kankanin lokaci. Haka kuma yakai irin wannan ziyara a yankin kanoma dake karamar hukumar Maru  yaji korafe, korafen da al'ummar wanan yanki suke dasu wanda hakan yasa aka dakatar da sarkin na Maru dakuma hakimin Kanoma bisa zarginsu da alaka da Yan bindiga, Wanda yake tsohuwar Gwamnati Bata taba irin wannan kokariba. A tsohuwar Gwamnatin data gabata ankashe mutum fiye da dubu biyar (5,000) anraunata fiye da mutum dubu goma anbiy...

Ban hana 'yan Shi'a yin shi'arsu ba - Buhari

Image
El-zazzaky Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce umarnin da kotu ta bayar na dakatar da kungiyar IMN bai hana mabiya Shi'a su gudanar da addininsu ba a kasar. Kalaman shugaban na zuwa ne bayan hukuncin wata kotu a Abuja, ranar Juma'a, da ya bayar da umarnin haramta Kungiyar IMN ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky kamar yadda gwamnati ta nema. Bayanan kotun sun nuna cewa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar ta IMN bayan ayyana ta a matsayin ta 'yan ta'adda, inda ta zarge ta da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi. Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya yi watsi da zargin cewa suna tayar da husuma, sannan ya shaida wa BBC lauyoyi da jagororinsu na nazari kan umarnin kotun domin fitar da matsaya. Tashin hankali ya kazanta a baya-bayan nan tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan kungiyar, wadanda ke zanga-zanga akai-akai tun bayan tsare shugabansu da gwamnati ta yi a shekarar 2015. Sai dai mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya shai...

Shi'a: Gwamnatin Najeriya za ta 'haramta' kungiyar IMN

Image
Aika wannan shafi Facebook   Aika wannan shafi WhatsApp   Aika Image caption Sheikh El-zakzaky ya ce ba zai fasa a bin da yake yi ba Gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'. Jaridar  Punch Newspaper  ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin a ranar Juma'a. Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a." Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya. "Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungi...

Dalilin kin sakin Sambo Dasuki da Ibrahim Zazzaky - Malami

Image
Shugaba Buhari da Abubakar malami Tsohon ministan shari'a kuma wanda ake tunanin za a sake ba mukamin, ya fadi dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki Kanal Sambo Dasuki da kuma Shiekh elZakzaky. Barista Abubakar Malami, wanda shugaba Buhari ya sake zaba a matsayin minista, yana cikin wadanda suka bayyana a gaban majalisar dattawa a ranar Juma'a domin tantance su. Batun yadda ya yi fassara da kuma bai wa shugaban kasa shawara kan wasu hukunce-hukuncen kotuna musamman wadanda ake ganin ba su yi wa gwamnati dadi ba, su ne suka fi jan hanakali a tambayoyin da aka yi masa. An tambayi tsohon ministan na shari'a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu amma kuma ake ci gaba da tsare da su. Malami ya shaida wa BBC cewa ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin 'yan Najeriya ba na wani mutum daya ba. Ya ce ...

TARIHIN MALAM ISAH ALI PANTAMI

Image
Dr. Isah Ali Pantami An haifi Malam Isah Ali Pantami ranar 20 ga watan goma (October) shekarar 1972 a garin Gwambe dake Nigeria, shekarunsa 46, sunan mahaifiyarsa Hajiya Amina Umar Aliyu, mahaifinsa Alhaji Ali Ibrahim Pantami. Yafara karatu a makarantar allo tareda hardar al qur'ani Mai girma, yashafe fiye da shekara hudu a makarantar allon kafin daga bisani asakashi primary a garin Pantami, yayi karatunsa na sakandiri a Goverment science Secondary schools dake Gwambe. Bayan kammala sakandiri yashafe shekara biyu Yana karatun addini kafin daga bisani ya halarci Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi, inda yasamu digirinsa ta daya data biyu (Bsc,Msc) a fannin Fasahar kwamfuta a shekarun 2003 da 2008, daga bisani kuma yaje Jami'ar Robert Gardon a Aberdeen dake kasar Scotland inda yasamu digirinsa ta ukku (PhD). Yashafe gabada daya rayuwarsa akan karatun addini Dana Zamani. Malaman dayayi koyon karatu wajensu sun hada da; Muhammad Umar fallata, Muhammad ibn al...

Yadda matashi ya kashe mahaifinsa mai shekara 70

Image
Yan sandan Nigeria Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar wa BBC cewa da misalin karfe 12 na ranar Talata ne dai matashin mai shekara 25 ya bi mahaifin nasa mai shekara 70 zuwa gona, inda ya sa kotar fartanya ya buge shi. SP Jinjiri ya kara da cewa an tarar da dattijon a kwance magashiyyan a gonar tasa, ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi zuwa asibiti, inda ya ce ga garunku nan. Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta Jigawa ta ce ta cafke matashin wanda ya tsere bayan ya 'tafka ta'asar' SP jinjiri ya ce bayan tambyoyi da suka yi wa matashin sun fahimci cewa yana cikin halin maye saboda haka ana kyautata zaton kwaya ce ta debe shi ya yi 'aika-aikar' Yawan kashe-kashe a tsakanin dangi a Najeriya Kusan za a iya cewa kisa a dangi, inda ake samun yanayin da mata ke kashe mai gida ko kuma mai gida ya kashe matar ko kuma dan uwa da 'yar uwa ko ma da ya kashe mahaifi ko mahaifiyarsa, ya dade y...

TakaiTaccen Tarihin Sadiya Farouk

Image
Sadiya Umar Farouk A ranar Talata ne Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yaturawa majalisar dattawa Sunayen Mutanen dayakeso yanada amatsayin Ministocinsa. Hajiya  Sadiya Farouk itace matar da Sunanta yafito daga jihar Zamfara, al'ummar jihar Zamfara sunaso Susan wacece Sadiya Farouk. Ga takaitaccen tarihinta; Anhaifi Sadiya Umar Farouk a karamar hukumar zurmi a Jahar zamfar, tayi karatun primary da secondary agarin Gusau, takammala secondary schools dinta a federal  government girls college (FGGC, Gusau). Daganan ta garzaya Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna ta karanci Business administration, ta kammala a shekarar 1998. Takuma yi degree dinta ta  biyu(Masters) a Fanni international affairs and diplomacy a shekara 2008 dakuma Business administration a shekara 2011 Duka a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Tayi bautar kasar ta (NYSC) a majalisar dokokin Nigeria a shekarar 2000, tayi aiki tareda kwamitin majalisar dattawa na jiragen sama. Takumayi aiki a...

Jerin Sunayen Sabbin Ministocin Nigeria

Image
Muhammadu Buhari ya fara fitar da sunayen sabbin ministocinsa. Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya fara wallafa sunayen a sahafinsa na Twitter a ranar Talata. Daga cikin sunayen da aka fitar zuwa yanzu akwai tsofafin minsitocinsa akwai kuma sunayen sabbin mutane da a baya ba sa cikin majalisar zartarwar shugaban. Sunayen sababbin ministoci  a karon farko Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom Alhaji Sabo Nanono - Kano Gbemi Saraki (Kanwar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki) - Kwara Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun George Akume - tsohon gwamnan - Benue Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa Sadiya Farouk - Zamfara Maryam Katagum - Bauchi Ramatu Tijjani - Kogi Sanata Olorunnibe Mamora - Legas Sunday Dare - Oyo Festus Keyamo - Delta Sharon Ikeazor - Anambra Sanata Tayo Alasoadura - Ondo Pauline Tallen - Filato Mustapha Buba Jedi Agba - Olamilekan Adegbite - Ogun Mohammed...