Ko Gwamna Ganduje zai jingine nadin sabbin sarakuna?
Gwamna Ganduje na Kano Kwamishinan shari'ah na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtari ya fada wa BBC cewa har zuwa daren ranar Juma'a, bai karbi wani umarni daga kotu (game da batun nada sabbin sarakuna da kirkirar karin masarautu na gwamnatin Kano) ba. Babbar kotun jihar Kano ce ta ba da umarnin cewa gwamnati da majalisar dokokin jihar su dakatar da duk wani mataki na kirkirar sabbin masarautu a jihar ta Kano har sai ta saurari karar da wasu 'yan majalisa suka shigar gabanta suna kalubalantar matakin yin dokar. "Ban san da kara ba, kawai dai yadda kuke ji a gari, (ni ma) haka nake ji a gari." Barista Ibrahim Mukhtari ya ce: "Ni ban ga oda ta kotu ba kowacce iri." Ya kara da cewa don haka ba za su ce komai a kai ba, har sai sun ga takardar kotu. Za dai a zuba ido a gani ko gwamnatin jihar Kano za ta dakatar da nadin sarakunan a ranar Asabar kamar yadda ta tsara bisa umarnin kotu, ko kuma za ta yi biris da umarnin ta ci gaba da shagulgulan bai ...