Posts

Showing posts with the label yansanda

Bazamu Bari akifar da Gwamnatin Buhari ba - 'Yan sanda

Image
Sufeton Yan sandan Nigeria Sifeton 'yan sandan, Muhammad Adamu a wani gargadi da rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na twitter, ya ce rundunar 'yan sanda ba za ta zura ido ga masu son kifar da zababbiyar gwamnati ba. Gargadin ya ce "rundunar 'yan sanda ta ga wani bidiyon da ke karakaina a soshiyal midiya wanda ya fito daga wata kungiya mai suna Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria and others', da ke tunzura 'yan Najeirya na gida da waje wajen shiga a dama da su a zanga-zangar yi wa gwamnatin Najeriya matsin lamba a ranar Litinin 5 ga watan Agusta da manufar kifar da gwamnatin." Rundunar da ta kara da cewa " Rundunar 'yan sanda na sanar da jama'a ba tare da shakku ba cewa wannan zanga-zangar daidai take da cin amanar kasa da aikin ta'addanci saboda haka rundunar ba za ta zura wa masu yunkurin yin hakan ido ba su tayar da zaune tsaye a kasa ba." Sifeto Janar ya kara da cewa "a...