Damar da nake da ita kan zabe ta kare - Atiku
Atiki Abubakar Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 na jam'iyyar adawa ta PDP, Ahaji Atiku Abubakar ya amsa cewa damar da yake da ita, domin bin kadin zabe a gaban kotu, ta riga ta kare. Ya ce hukuncin, wani bangare ne na kalubalen dimokradiyya, wanda ya zama dole su tunkara a matsayinsu na kasa. Jagoran adawar na wannan bayani a matsayin martani bayan hukuncin Kotun Kolin kasar wadda ta yi watsi da karar da ya daukaka. Alkalan Kotun Kolin dai sun yi watsi da daukaka karar bisa dalilan rashin makama, inda kuma suka ce nan gaba za su bayar da dalilan da suka dogara da su. Dan takarar na PDP ya yi wannan jawabi a shafinsa na twitter bayan hukuncin kotun kolin na ranar Laraba. Alhaji Atiku Abubakar ya ce hanyar shari'a da ya dauka duk da cewa ta zo karshe, a saboda haka duk wata dama da yake da ita ta kare. Alhaji Atiku ya kuma ce an yi adalci a hukuncin ko ba a yi ba alkalanci ya rage wa 'yan Najeriya inda ya ce a amatsayinsa na wanda ya yi imani da tsari...