Posts

Showing posts with the label yantakara

Jahilci ne yasa al'ummar Dogon Kade yin Zanga Zanga

Image
Gwamna Bello Matawalle Abinda al'ummar yankin jimrawa gundumar dogon kade karamar hukumar kaurar namoda sukayi  ajiya nadauko gawa biyu a babur zuwa gidan Gwamnatin jihar Zamfara jahilci ne. Saboda Kai hare hare ba yaune akasaba ba, kuma ita wannan Gwamnati gadar abintayi, kuma duka har yau Bata cika wata 2 akan mulki ba. Kuma wannan kauyen ansha kashemasu mutane tun alokacin waccen tsohuwar Gwamnati wacce itace silar wannan matsala  Amma basu taba maganaba. Kawai abin lura anan shine Wasune wadanda basuson Zamfara tazauna lafiya sukayi amfani da jahilcin wadannan mutane suka sasuyin wannan aiki  saboda sukawo cikas ga kokarin  da Gwamnati keyi nakawo Zaman lafiya madorewa a Jaharmu ta Zamfara. Gwamnan jihar Zamfara Hon. Bello Muhammad (Matawallen Maradun) tun lokacin dayakama aiki Zamafarawa sunshedi lallai wanan Gwamna aiki yazoyi ba Wasa ba, lura da irin namijin kokarin da yake.  Matsalartsaro itace babbar matsalar data addabi al'ummar Jahar Zamfara,...

Zaben da muka yi mun yi kura-kurai - Gwamna Yari

Image
Gwamnan Zamfara mai Barin Gado Gwamnan Zamfara mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da hukuncin kotun koli tare da yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri. A yayin da yake jagorantar shan ruwan azumin ramadan na karshe tare da kwamishinoni da manyan kushoshin gwamnatinsa a gidansa da ke Talatar Mafara gwamnan ya ce "mun aminta kuma mun yadda da hukuncin Ubangiji." A ranar juma'a ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fitar da gwani ba wanda hakan ya yi sanadin soke kuri'un da jam'iyyar ta samu a dukkanin kujerun da ta lashe a zaben 2019 a jihar. Hukumar INEC kuma ta tabbatar da 'yan takarar jam'iyyar PDP da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben na gwamna da na 'yan majalisar Tarayya da na jiha. Da yake jawabi, Gwamna Yari ya amsa cewa zaben da aka yi akwai kura-kurai a ciki, inda ya ce sun yadda da hukuncin kotun koli, "wannan tsari ne wanda Allah ya riga ya tsara haka....