'Yan gudun hijirar 25,000 ne suka dawo gida a Zamfara - Hukumar agajin gaggawa
Gwamna Bello Matawalle Adadin mutane 25,000 da rikicin 'yan fashi ya ritsa da su a jihar Zamfara ya zuwa yanzu sun koma garuruwansu sakamakon kokarin wanzar da zaman lafiya da gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi. Alhaji Sanusi Kwatarkwashi, Sakataren zartarwa na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Zamfara ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Gusau ranar Juma'a. Kwatarkwashi ya bayyana cewa jihar ta rubuta 37,000 'Yan gudun hijira a cikin tsananin zafin na masu yin garkuwa da mutane. Ya ce, wadanda suka dawo sun koma kan sana'arsu ta yau da kullun na noma, kiwo dabbobi da sauran ayyukansu. Kwatarkwashi ya ce sauran 'yan gudun hijirar 12,000, 000 sun kasance a Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto da kuma wani bangare na Jamhuriyar Nijar. Ya ba da tabbacin cewa an kafa gwamnatin jihar don mayar da su garuruwansu kamar yadda kwanciyar hankali ya dawo a jihar Na yi imanin dukkan 'yan gudun ...