Posts

Showing posts with the label nigeria

Jerin tafiye tafiyen da shugaba Buhari yayi cikin shekara Hudu da Rabi

Image
Shugaba Muhammad Buhari Idan akwai wani batu da aka tayar da kura a makon nan, shi ne na tashin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Saudiyya domin halartar wani taron kasuwanci, inda daga nan zai wuce zuwa birnin Landan, kafin daga bisani ya koma Najeriya a ranar 17 ga Nuwamba. A ranar Asabar din nan ne ake sa ran Shugaba Buharin zai bar kasar Saudiyya zuwa Birtaniya domin kai wata ziyarar radin-kai inda zai kwashe kwana 17. Idan har Buhari ya koma Najeriya a ranar 17 ga watan Nuwamba, to lissafi zai kama kwanaki 425 ke nan shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekara hudu da rabi na mulkinsa. Gajerin tafiyeta da Sugaba Huharin uayi 2015 3 Yuni - Niamey - Niger - Taron koli kan Boko Haram (tafiyar Buhari kasar waje ma7ko guda bayan shan rantsuwa) 4 Yuni - N'Djamena - Chad - Ziyarar aiki 7 - 8 Yuni - Munich - Germany - Taron koli na kasashen G7 na 42 12 - 13 Yuni - Johannesburg - Afirka ta Kudu - Taron Tarayyar Afirka na 25 19 - 23 Yuli - Washington, D.C. ...

Buhari ya sa hannu kan kasafin kudin 2019

Image
Shugaba Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.91. A watan Disambar 2018 ne dai Shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar dokokin kasar kasafin na naira tiriliyan 8.83. To sai dai majalisar ta kara naira biliyan 90 da miliyan 300 inda ta amince da kasafin na naira tiriliyan 8.91. An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana. Har wa yau, an gina kasafin bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan kowace ganga, da kuma kan farashin canji N305 kan dala daya. Idan za a iya tunawa dai Shugaba Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019. Shugaban ya ce wannan shi ne jawabin gabatar da kasafin kudi na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas. Wannan ne kuma kasafi na karshe da shugaban ya gabatar a wa'adin mulkinsa na farko da ke karewa ranar Laraba. A jawab...

Ya kamata ministocina su yi alfahari da kansu – Buhari

Image
Shugaba Buhari da Ministocinsa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa ministocinsa cewa ya kamata su yi alfahari da kasancewarsu wani bangare na "gwamnati mafi sanin makama". Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron majalisar ministoci ranar da ake yi duk ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja. Wannan dai shi ne zaman da shugaban ya yi a majalisar zartarwarsa na karshe da ministocinsa. Sai dai shugaban ya ba su damar ci gaba da aiki har zuwa 28 ga watan Mayu, inda za su mika takardar ajiye aiki ga sakataren gwamnati Boss Mustapha, kwana daya kafin a rantsar da sabuwar gwamnatinsa a mako mai zuwa. Da yake jawabi a cikin dakin taron, Shugaba Buhari ya ce sunayen ministocin ya shiga cikin tarihin Najeriya, wanda hakan abin alfahari ne. "Kowannenku yana da wata baiwa ta musamman kuma mu ne hoton Najeriya da muke fatan ginawa. Kasa mai kabilu da dama wadda kowanne dan kasa yake da 'yancin fadar albarkacin bakinsa. "Ya kamata ku yi alfahari da k...

Laifin gwamnati ne matsalar tsaro a Najeriya- PDP

Image
Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce matsalolin da al'ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya sa rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki. Sanata Umaru Tsauri, sakataran kasa na jam'iyyar PDP ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC. Ya ce rashin fadar gaskiyar lamurra game da halin da kasa ke ciki daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka jefa kasar cikin halin rashin tsaron da take ciki. An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan sa-kai da masu satar mutane Birtaniya za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta'addanci Ba mu gaza ba wajen yaki da masu satar mutane - Dambazau Ya ce "babu abin da ya jawo wannan matsala illa gwamnati ta ki yarda ta fadi wa mutane gaskiya cewa wannan abu na faruwa, kuma a dauki mataki." Ya kuma ce aikin gwamnati ne ta gano wadanda ke da hannu cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar tsaro a Najeriya, ba jama'ar kasar ba. Sanata Umaru Tsauri ya ce halin da Najeriya ...

Mun gama da masu satar mutane – Sufeton 'Yan Sandan Najeriya

Image
Sufeton 'Yan sandan Nigeria Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce jami'an tsaro sun ci galaba a kan masu satar mutane don neman kudin fansa a kasar. Sai dai ya ce akwai sauran aiki a gaba "don ba wai gaba daya muka gama da su ba. Amma mun ci galaba a kansu sosai-sosai." Babban sufeton ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kawo karshen matsalar satar mutune a kasar. Ya bayyana hakan ne lokacin wani taro na shugabannin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da ke yankin Afirka ta yamma (WAPCCO) a makon jiya. Kazalika ya musanta batun da wasu masu sharhi suke cewa tsaron cikin gidan kasar ya gagari 'yan sanda. "Sojoji suna aiki da 'yan sanda ne don su taimaka, amma duk inda ka tafi a duniya idan dai maganar tsaro na cikin gida ne 'yan sanda ne ke kan gaba." Ya ce dukkansu suna yi wa gwamnati ne aiki, "kuma abin da dan Najeriya ke so shi ne zaman lafiya." "Aiki ba wai ya gagari 'ya...

Yadda za ku kauce fadawa rikici da 'yan sandan Najeriya a kan hanya

Image
Yin murmushi da da'a da kuma gudun yin fada da dan sanda na cikin abubuwan da ke taimakawa direba a duk lokacin da ya zo gaban shingen bincike na 'yan sanda kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter. Ba a bayyana takamaiman dalilin da ya sa rundunar 'yan sandan ta wallafa wadannan shawarwarin amma ana ganin an wallafa ne sakamakon wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta na wani dan sanda na da ke cin mutuncin wani direba. A cikin bidiyon, an nuna wani dan sanda inda ya bukaci a ba shi cin hancin naira 4,000 saboda abin da direban ya yi niyyar ya ba shi bai kai hakan ba. Irin wadannan lamuran sun sha jawo a harbe direbobi su mutu sakamakon kin bayar da kai bori ya hau. 'Yan sandan ba su yi magana a kan karbar cin hanci ba, amma a shawarwarin da suka bayar na mu'amala cikin mutunci da 'yan sanda a yayin da aka same su a gaban shingen bincike na kanya sun bayar da shawarar cewa: ''A lura da suna ko lamba ko kuma motar jami'...

Kalaman Buhari kan tsaro sun jawo ce-ce-ku-ce

Image
Sufeton 'Yan sanda, Shugaba Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban sufeton 'yan sanda kasar na kokari matuka wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar. Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo kasar bayan kwashe kwanaki 10 a birnin Landan. Shugaban ya ce "ga duk wanda ya san sufeton 'yan sanda to zai fuskanci ya rame sosai saboda tsabar aikin da yake yi." Hakazalika a lokacin da dan jaridar tashar talabijin din kasar NTA ya yi masa tambaya kan kafa sabuwar gwamnati, Buhari ya amsa da cewa "ba zan ce komai a kai ba." Sai dai wadannan kalaman nan shugaban sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kasar. Wasu suna ganin bai kamata shugaban ya yi su ba, ganin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a kasar da kuma yadda ake satar mutane don neman kudin fansa ba dare, ba rana a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna. Cikin kwanaki da shugaban ya shafe baya kasar an samu matsaloli tsaro da dama da garkuwa ...

'Yan Najeriya na kewar 'Yar Adua bayan Shekara 9 da mutuwarsa

Image
Margayi Ummaru Musa 'Yar adua Jama'a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da ta'aziyyar rasuwar shugaban kusan shekaru 9 kenan bayan rasuwarsa. Jama'a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi kan wasu abubuwan alheri da ya shuka a lokacin mulkinsa da suka hada da rage kudin man fetur, karin albashi musamman ga 'yan sanda. Haka ma dai ana ci gaba da tunawa da shi wajen irin rawar da ya taka wajen ganin cewa an samu sulhu da tsagerun yankin Niger Delta a wancan lokaci inda ya samar masu da sana'o'i da tallafin karatu da dai sauransu. Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ba a bar shi a baya ba wajen tunawa da Marigayi 'Yar'adua domin a shafinsa na Twitter ya tuna da irin ayyukan da ya gudanar na gina kasar a wancan lokaci. Rasuwar Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya. Kafin rasuwarsa, ya...

''Yan fashi sun kashe sama da mutum 30 a Zamfara'

Image
Hanyar Dan Sadau a Zamfara Sarkin Kudun Dan Sadau a jihar Zamfara ya shaida wa BBC cewa 'yan fashin daji sun kashe sama da mutum 30 lokacin da suka auka wa kauyen Dan-Gurgu na masarautarsa tare da jikkata karin wasu 12. Alhaji Hussaini Umar ya ce dukkan mutanen da abin shafa maza ne, wadanda aka far wa a lokacin da suke haramar tafiya gonakinsu wayewar garin ranar Asabar. Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammed Shehu ya ce mutum goma aka kashe yayin wannan hari, tare da jikkata karin wasu hudu. Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan fashin daji, wadanda kan far wa kauyuka, su kashe mutane, tare da kona gidajensu har ma da dukiyar da suka mallaka. Ko da yake da farko sun fara ne da satar mutane, inda sukan rike su har sai dangi ko makusantansu sun biya kudin fansa. Masarautar Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru ta yi makwabtaka da yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, wanda ya yi kaurin suna ...

An haifi jaririya mai kai biyu a Sokoto

Image
Jariri mai kai biyu An haifi jaririyar mai kai biyu a asibitin General Hospital wanda ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato. Mahifiyar jinjirar ta isa asibitin ne da misalin karfe biyar a ranar Alhamis din da ta gabata bayan da ta shafe sa'o'i tana nakuda a gida, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Wata jami'an asibitin ta gano cewa matar ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda jinjirar ta zo da kaffafu maimakon da kai, sai ta bukaci taimakon likitoci a asibitin. Likitocin ne suka gudanar da bincike kan matar kuma suka gano cewa jaririyar ta riga ta mutu saboda dadewar da matar ta yi tana nakuda kafin ta je asibitin. Daya daga cikin likitocin da suka duba matar, Dokta Malami Muhammad Gada ya ce sun fuskanci matsaloli da dama wajen kokarin fida jinjirar saboda yadda kan ta yake da nauyi. ''Matar ba ta taba zuwa awon ciki ba lokacinda take da juna biyun, lamarin da ya janyo ba a iya gane yanayin jinjirar ba da wuri,'' in ji shi. Image ...

An kashe mutum 3,500 a Zamfara a shekara biyar

Image
Gwamna Abdul'aziz Yari An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wasu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammad shinkafi ya shaida wa BBC. Ya ce alkalunma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na kasar gona. Farfesan ya ce sun tantance hakan ne saboda duk lokacin da 'yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura tawaga a kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya. Har ila yau ya ce akwai mutane da dama da rikicin ya raba da muhallansu. Ya kuma ce rikicin ya fi shafar harkar noma. Ya ce suna ba jami'an tsaro dukkannin goyon bayan da ya dace wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar. A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya ta dakatar da aikace-aikacen hakar ma'adanai a jihar. Ko mene ne dalilin dakatarwar? Adamu ya ce an yi hakan ne "bisa la'akari da bayanan...

Dalilin da ya sa na fadi zabe – Gwamnan Bauchi

Image
Gwamnan Bauchi Dan takarar jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana wa BBC dalilin da ya sa ya fadi zaben gwamnan jihar. A wata hirar da ya yi da BBC a Abuja ranar Talata, gwamnan ya ce Allah ne ya san dalilin da ya sa ya fadi zaben. Sai dai ya ce ya ci zabe a yawancin kananan hukumomin jihar, "idan ban da guda biyu wadanda aka yi aringizon kuri'u," a cewarsa. "Don haka sakamakon zaben ba ya nuni da cewa al'ummar jihar ba sa sonmu, don mun yi abin so. Idan aka shiga lungu da sako, za a ga wani aiki da gwamnatin APC ta yi," in ji shi. Gwamnan ya ce tuni ya taya wanda ya lashe zaben murna, kuma ya bukaci ya ja hankalin magoya bayansa yayin da suke murnar cin zabe domin "kada a tayar da hankalin jama'a." Har ila yau, ya ce ya yi farin ciki yadda aka gudanar da zabukan ba tare da an samu tashe-tashen hankulan jama'a ba. "Allah ne ke ba da mulki ga wanda yake so, kuma shi ne mai karba da...

Gwamnan Bauchi ya taya Bala Muhammad murna

Image
Sanata Bala Muhammad Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya taya zababben gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad murnar cin zaben jihar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter. Bala Muhammad ya doke gwamna mai ci ne Muhammed Abdullahi Abubakar dan takarar jam'iyyar APC, kamar yadda hukumar zabe INEC ta bayyana. PDP ta lashe zaben ne da kuri'a 515,113, yayin da APC da ke mulki a jihar ta samu kuri'a 500,625 Sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa ne kadai dama ya rage, kuma PDP ce ta lashe karamar hukumar inda ta samu kuri'a 39,225, yayin da APC ta samu kuri'a 30,055. An ta kai komo zuwa kotu bisa sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa musamman tsakanin hukumar INEC da kuma jam'iyyar APC a jihar ta Bauchi, bayan da jam'iyyar ta kai hukumar kotu inda ta bukaci a dakatar da tattara sakamakon Tafawa Balewa. A ranar Talata ne dai kotun ta dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa a lokacin da hukumar ke dab da fara tattara sakamakon zaben. ...

TAMBUWAL YA LASHE ZABEN SOKOTO

Image
Gwamna Aminu waziri Tambuwa Dan takarar jami'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya lashe zaben Sokoto da kuri'u 512,002, bayan da ya doke Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC. Ahmed ya samu kuri'u 511,660 inda Tambuwal ya tsallake rijiya da baya da bambancin kuri'u 342. A zaben da  aka kammala a ranar Asabar, APC ta samu kuri'u 25,515 sai kuma jam'iyyar PDP wadda ta samu kuri'u 22,444. A yanzu haka dai Aminu Tambuwal ne ya lashe zaben da aka kammala. Ranar Asabar 9 ga watan Maris ne aka gudanar da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a Najeriya. Kuma an samu tsaiko a wasu jihohi inda sakamakonsu bai kammalu ba, kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da kammala karashen zaben ranar 23 ga watan Maris din. Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da zabensu bai kammalu ba saboda gibin da ke tsakanin 'yan takarar biyu bai kai yawan kuri'un da aka soke ba, inda aka soke zabe a rumfunar zabe 135...

Abinda kwankwaso yace gameda zaben kano

Image
Sanata Rabi'u Musa Kankwaso Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaben gwamna da za a kammala a jihar Kano zai tabbatar ko kuma rushe darajar gwamnati da hukumar zaben kasar INEC. Kano na daga cikin jihohi biyar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce za ta gudanar da zaben cike gibi a cikinu, a ranar 23 ga watan Maris. Wannan mataki ya zo ne bayan da hukumar ta INEC ta ce zabukan jihohin ba su kammala ba saboda soke sakamakon wasu mazabu, wadanda yawan kuri'unsu suka zarce tazarar da ke tsakanin 'yan takara biyu mafiya yawan kuri'u a zaben na gwamna. A tattaunawar sa da BBC gabanin zaben, Sanata Kwankwaso ya ce zaben na jihar Kano na daukan hankulan al'ummar Najeriya da ma wadansu kasashe. Ya kara da cewa 'wannan shi zai tabbatar da darajar ita kanta hukumar zabe da gwamnati, ko kuma ya ruguje ta.' A zaben gwamna da aka gudanar na jihar Kano, ranar 9 ga watan Maris, jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da yawan kuri'a, in...

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Image
Shugaba Muhammadu Buhari A shekarar 2003 da shugaba Buhari yafara tsayawa takara, jahar Zamfara sunyimai ruwan kuri'u a jam'iyarsa ta APP kuma itace jamiyar dake mulki a jahar Zamfara a wancen lokacin haka a 2007 bayan sauya sunan jam'iyar daga APP zuwa ANPP al'ummar Zamfara sunsake marama Buhari baya hakama a 2011 bayan barin jam'iyar ANPP yakoma CPC al'ummar Zamfara sun mara masa baya har yalashe zabe ajahar duk da ba itace jam'iyar dake mulkiba a jahar ba a wancen lokacin, haka kuma a 2015 bayan dunkulewar manyan jam'iyun adawa waje daya suka samarda jam'yar APC kuma suka aminta Shugaba Buhari Yatsaya masu takara, al'umma Zamfara basugajiba suka sake marawa shugaba Buhari baya har Allah yakaishi ga samun nasarar zama shugaban kasar Nigeria, bakomai yasa al'ummar zamfar ke goyon bayan Buhari ba sai saboda Gaskiya da rikon amanar da akasanshi dasu. Amma duk da wannan namijin kokarin da Al'ummar Zamfara sukayiwa Shugaba Buhari b...

ANYI KUSKURE WAJEN DAGE ZABEN BAUCHI- INEC

Image
Shugaban hukumar Zabe Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na mazabu da rumfunan zabe domin hada sakamakon karamar afawa Balewa a zaben gwamna da na 'yan majalisar dokoki na jiha. Hukumar ta nada sabon jami'in zabe da zai ci gaba da tattara sakamakon, wanda kuma zai maye gurbin tsohuwar jami'ar tattara sakamakon wacce ta janye daga aikin saboda barazana da tace tana fuskanta. A makon jiya ne hukmar zaben ta Najeriya INEC ta bayyana cewa zaben jihar Bauchi bai kammala ba, kuma za a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, saboda rashin samun sakamakon zaben kamar yadda dokokin zabe suka tanada, bayan tashin hankali yayin tattara sakamakon. INEC ta ce za ta yi amfani da kwafin takardun da aka rubuta sakamakon zaben a kansu a mazabu, wadanda daga nan za a samu sakamakon karamar hukumar. Sannan hukumar ta ce gano cewa akwai kuskure wajen lissafin kuri'un da aka soke a rumfuna hudu a karamar hukumar Ningi...

ABUBUWAN DA YAN ZAMFARA ZASU TUNA KAFIN SUKADA KURI'A

Image
Gwamna Abdul'aziz Yari na Zamfara Jefa kuri'a abune mai mahimmanci amma yakamata kasan wazaka jefama kuri'ar. Duk dan jahar Zamfara yakamata yatuna wadannan abubuwan kafin yajefa kuri'ar sa; 1.  Cikakkar matsalar rashin tsaro ga jaha 2.  Kasa biyan ma'aikata 1400 albashi dasuka shafe wata 54 suna aiki 3.  Kasa biyan mafi karancin albashi da rashin karin girma ga ma'aikata tsawon shekara 8 4.  Dakatar da koyarda ayukan hannu ga matasa da mata marar aikinyi tsawon shekara 8 5.  Tabarbarewar harakar kiwon  lafiya 6. Rashin kayayyakin more rayuwa nazamani da rashin ayukan cigaba ga jaha 7.  Rashin yancin fada aji 8. Rashin bada dama ga yantakarar da mutane keso 9.  Jefa alqur'ani maigirma cikin bahaya (Masai) 10 Kasa biyan kudin WAEC da NECO akan lokaci ga daliban dasuka kammala secondry 11.  Dakatar da biyan kudin schorlarship ga daliban gaba ga secondry 12.  Sace sacen mutane dakuma kashesu basuji basu gani ba...

KIRA NA MUSAMMAN GA YAN TAKARAR JAM'IYUN ADAWA NA JAHAR ZAMFARA

Assalamu alaikum, Al'amarin siyasar Zamfara yana matukar bani tsoro lura da irin yanayin tabarbarewar harkar tsaro a jahar nan. A fili take cewa gwamnatin APC mai mulki bata damu da halin da al'ummar Zamfara suke ciki ba, tafi damuwa da sha'anin siyasar ta bisa kula da kare rayukan mutane da dukiyoyinsu saboda haka a tunani na Insha-Allahu canza gwamnati shikadai ne mafita ga al'ummar jahar Zamfara amma dole sai su mutanen Zamfara sun tashi sunyi dagaske koda Allah zai taimakesu lura da irin taurin kai da nuna halin a mutu ko ayi rai akan rasa wannan mulki da gwamna mai barin gado yake dashi. Saboda haka naga ya dace inyi wannan kira ga manyan yan takararmu na jam'iyun adawa, kamar Hon. Bello Matawalle, Hon. Sani Abdullahi Wamban Shinkafi da Sanata Sa'idu Muh'd Dansadau da cewa su dibi halin da jahar Zamfara take ciki su ajiye adawar siyasa su hadu su marawa daya daga cikinsu baya domin ceto jahar Zamfara daga bala'in da take ciki. Dalilin d...