'Yan Najeriya na kewar 'Yar Adua bayan Shekara 9 da mutuwarsa
Margayi Ummaru Musa 'Yar adua Jama'a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da ta'aziyyar rasuwar shugaban kusan shekaru 9 kenan bayan rasuwarsa. Jama'a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi kan wasu abubuwan alheri da ya shuka a lokacin mulkinsa da suka hada da rage kudin man fetur, karin albashi musamman ga 'yan sanda. Haka ma dai ana ci gaba da tunawa da shi wajen irin rawar da ya taka wajen ganin cewa an samu sulhu da tsagerun yankin Niger Delta a wancan lokaci inda ya samar masu da sana'o'i da tallafin karatu da dai sauransu. Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ba a bar shi a baya ba wajen tunawa da Marigayi 'Yar'adua domin a shafinsa na Twitter ya tuna da irin ayyukan da ya gudanar na gina kasar a wancan lokaci. Rasuwar Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya. Kafin rasuwarsa, ya...