TARIHIN MALAM ISAH ALI PANTAMI
Dr. Isah Ali Pantami An haifi Malam Isah Ali Pantami ranar 20 ga watan goma (October) shekarar 1972 a garin Gwambe dake Nigeria, shekarunsa 46, sunan mahaifiyarsa Hajiya Amina Umar Aliyu, mahaifinsa Alhaji Ali Ibrahim Pantami. Yafara karatu a makarantar allo tareda hardar al qur'ani Mai girma, yashafe fiye da shekara hudu a makarantar allon kafin daga bisani asakashi primary a garin Pantami, yayi karatunsa na sakandiri a Goverment science Secondary schools dake Gwambe. Bayan kammala sakandiri yashafe shekara biyu Yana karatun addini kafin daga bisani ya halarci Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi, inda yasamu digirinsa ta daya data biyu (Bsc,Msc) a fannin Fasahar kwamfuta a shekarun 2003 da 2008, daga bisani kuma yaje Jami'ar Robert Gardon a Aberdeen dake kasar Scotland inda yasamu digirinsa ta ukku (PhD). Yashafe gabada daya rayuwarsa akan karatun addini Dana Zamani. Malaman dayayi koyon karatu wajensu sun hada da; Muhammad Umar fallata, Muhammad ibn al...