Duba kaga Hasarar da Zamfara tayi Zamanin Mulkin Abdul'aziz Yari
Abdul'aziz Yari A cikin shekara takwas 8 na mulkin tsohon Gwamna Abdul'aziz Yari, alkaluma sunnuna cewa ankaiwa kauyuka 800 hari, ankashe fiye da mutun dubu biyar 5,000, anraunata fiye da mutum dubu goma 10,000, Sannan an barnata tareda lalata filayen noma dazasu Kai hekta 15,000, anbiya kudin fansa dazasu haurama naira biliyan goma 10,000,000,000, saboda anyi fansar mutum fiye da dubu goma 10,000, Sannan akwai kananan yara da aka kashewa mahaifa aka maidasu marayu da zasukai dubu goma 10,000, akwai matan aure da aka kashewa mazaje anka maidasu zawarawa da yawansu zaikai dubu hudu 4,000. Wannan dinbin Hasara shiyajefa Jihar Zamfara cikin wani mummunan yanayi na daidaicewa, Kuma rikon sakaina Kashi da halin ko inkula da Tsohon Gwamna Abdul'aziz Yari yayi da Jahar ne yajefata cikin wannan Bala'in. Saboda acikin wata biyu na mulkinsa Gwamna Matawalle sanadiyar sulhun dayayi da barayin shanu masu satar mutane ankubutar da rayukan mutum fiye da dari ukku 300...