Posts

Featured Post

Gwamna Matawalle ya aminta da Gina cibiyoyin kula lafiya 14 da sake Gina sakatariyo 14 a Zamfara

Image
Gwamna Bello Matawalle Mai Girma, Gwamnan jihar Zamfara Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) ya amince da fara ayyukan gaggawa a ginin cibiyoyin kula da lafiya 14 tare da sabunta wasu daga cikin da shugabannin kananan hukumomin na karamar hukumar. Yarda da gwamnatin tayi shine inganta daidaiton cibiyoyin kula da lafiya na jihar a dukkan matakai musamman a yankunan karkara kuma suna da asibitoci na zamani da wuraren da zasu samarda ingantaccen kulawar lafiya ga mutanen yankin musamman mata da yara. Sauran amincewar da gwamnan yayi ya hada da na samar da wuraren zama masu dacewa ga ma’aikatan kananan hukumomi wadanda za su zama daki biyu zuwa uku wadanda za su kasance a dukkanin kananan hukumomin 14 na jihar tare da inganta rayuwar ma'aikatun karamar hukuma da iyalansu. Gwamnan ya kuma amince da sake gina dukkan sakatariyar kananan hukumomi 14 da za su kasance iri guda domin samar da yanayi mai kyau da kuma samar da yanayi ga ma'aikatan ka...

Wanene Muhammad Mursi

 MUTUNA DA MTUMIN DAYA KARE MARTABAR ANNABI S.A.W A GABAN MAKIYANSA: Shine Shugaban Qasar Da Yaje Majalisar ‘Dinkin Duniya Agaban Yahudawa Yabaiwa Annabi (S.A.W) Kariya.   Shine Shugaban Qasa Na Farko Acikin Shugabannin Qasar Egypt Da Yaja Sallah A Masallacin Annabi (S.A.W) Madina, Shine Shugaban Qasar Da Ya Bud’ewa Falatsinawa Iyakar Qasar Egypt Domin Zalincin Da Yahudawa Keyi Musu, Shine Shugaban Qasar Da A Lokacinsa Malamin Addini, Hafizin Qur’ani, Kuma Qwararran Engr A Fannin Boko, Shine Shugaban Qasar Da Yafito Da Malamai Da Duk Wanda Aka ‘Daure Bisa Zalinci A Mulkin Husnul Mubarak, Shine Yayi Qoqarin Tsarin Qasar Egypt Ya Tafi Daidai Da Tsarin Musulunci, Shine Wanda Larabawa Masu Qawance Da America Suka Had’a Baki Da Isra’el Wajen Kifar Da Gwamnatinsa, Shine Shugaban Qasar Da Yayi Shahada A Prison A Hannun Maqiya Addinin Allah, Shine Shugaban Qasar Da Aka Hana Y’an Uwansa, Da Masoyansa Su Sallaci Gawarsa. An Haifeshi  20/8/1951, Yazama Shugaban Qasa 30/6/2012, Anyi ...

Yakin Taliban

Image
  'YAN TALIBAN  (Don Allah a karanta a natse kuma a karanta gaba daya) Sun rayu a Æ™asar Apghanistan Dalilin faruwar wannan Ƙungiya shine:  Bayan Æ™asar Russia ta nemi sulhu tsakaninsu da Æ™asar Apghanistan akan yaÆ™in da sukayi shekaru sama goma suna gwazwa wato Æ´an mujahid da akafara a 1979-1989 bayan Æ™asar ta Rasha batayi nasara ba inda Tattalin Arzikin kasar yayi kusa rushewa inda tayi hasarar manyan kudade makuddai tayi hasarar makamai, toh bayan kasar Saudi Arabia tayi sulhu. Sai faÉ—an yakoma tsakanin Æ´an Æ™asar ta Apghanista suna kisan juna da kansu yazama babu Shugaban Æ™asa, babu Gwamna, babu Chairman babu Sarki ko Minista babu wani shugaba a Æ™asar kowa yanda yaga dama yakeyi ko Malamai masu bada shawara babu. kasar ta koma In anarchy babu shugabanci kowa ta kansa ya ke mai karfi ya buge marar karfi, babu inda zaka kai kara babu Kotu. A wannan lokacin sai mutanen Æ™asar Russia wadanda kasar ta Apghanistan tayi yaki dasu akayi sulhu suka fara shigowa suna ta'addanci ga '...

Falala da Bayani gameda kwanaki goma na farkon Dhul-Hajji

Image
Hadisin manzon Allah (SAW) ya tabbatar da cewa babu wani aikin ibada da yafi girman daraja fiye da a cikin kwanaki goma na farkon watan Dhul Hajji.  Imamu dabarani yaruwaito cewa Manzon Allah (s a w) yace; acikin kwanakin shekara akwai wasu kyaututuka na ubangiji, kuyi kokari kusamesu, Yana yuyuwa idan wani budi yasami dayanku acikinsu to har abada bazai sake tabewa ba.  Gakadan daga cikin Abu buwan da Ranakun suka kunsa. 1) Allah ya yi rantsuwa da kwanaki goman farko na Dhul-Hijja a cikin suratul fajari sura ta 89 aya ta 1-2. 2) Sune kwanakin da ake kira “AYYAMIN MA’ALUMAT” (kwanaki sanannu) : Allah yayi umurni ga muminai da su ambace sa a cikin kwanaki sanannu (Al-Haj:28) ayi zikiri saboda ni'imar Allah na dabbobin da ake yankawa na Hadaya da Layya. 3) Wadan nan kwanakin suna cikin arba'una na Musa Wanda Allah kecewa; katuna lokacin damukayi na haduwa, bayan cikar kwana 30 nafarko ubangiji yacemsa Yakoma yacika 10, wadannan sune kwanaki goma da akace annabi Musa yacika. 4) A...

Abubuwa 10 masu mahimmanci a kwanaki 10 na karshen Watan Ramadan

Image
A daren Lailatul Qadri da ke goman karshe na watan azumin Ramadan ne Allah ubangiji ya saukar da Alkur'ani mai girma, abin da ya sa Musulmi suke neman dacewa da wannan daren. Duk da cewa babu tabbacin wane dare ne aka ware cewa shi ne daren na Lailatul Kadri, amma hadisai da malamai sun nuna cewa daren yana wakana ne a mara ta karshen kwana goma na watan Ramadan. Dararen mara dai kan fara tun daga daren 21 da daren 23 da 25 da 27 da kuma 29. Hakan ne ma ya sa wasu Musulmin yin tsumbure dangane da ibadun da ake son yi wato idan sun yi wannan dare sai su huta a wani daren inda za su sake kaimi a daren mara na gaba. To sai dai malamai sun ce ba a yi wa ubangiji wayo, inda suke shawartar masu neman dacewa da su raya dukkanin daren goman karshen azumin Ramadan: Dr Bashir Aliyu Umar wanda shi ne limamin masallacin Alfurqan da ke birnin Kano ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Kadri, kamar haka: 1. Niyyar neman yardar Ubangiji 2. Neman...

Tarihin direban taxi dayazama Gwamna a Nigeria

Image
Gwamnan jihar Borno A ranar Laraba 29 ga watan Mayun 2019 ne aka rantsar da Babagana Umara Zulum a matsayin gwamnan jihar Borno, bayan ya ci zabe karkashin jam'iyyar APC, inda ya gaji Kashim Shettima. Jama'a da dama sun yi shaidar Babagana kan cewa ba mutum ba ne wanda yake son kyalkyalin kayan duniya ko kuma tara makudan kudi, ganin irin damar da ya samu ta tara abin duniya a matakai daban-daban bayan ya sha gwagwarmayar rayuwa. A baya-bayan nan tauraruwar gwamnan na haskawa a Najeriya, inda ake yawan yabon sa da jajircewa da nuna tausayin talaka, musamman halin da mutanen jiharsa ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram. Shin wane ne Babagana Umara Zulum? BBC ta yi nazari kan tarihinsa. Rayuwarsa An haife shi a ranar 26 ga watan Agustan 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a garuruwan Mafa da Monguno tsakanin 1975 zuwa 1985. Tun a lokacin da yake dan aji biyar a sakandare, Babagana ya bayar da himma wajen far...

Nasha alwashin karbo Naira biliyan 90 hannun Yari: Matawalle

Image
Gwamnan jihar Zamfara Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi alwashin dawo da sama da N90bn daga tsohon gwamna Abdulaziz Yari wanda ake zargin ya karkatar da shi ta hanyar hauhawar farashin kwangila. Matawalle, wanda ya yi jawabi a lokacin gabatar da rahoton wucin gadi daga kwamitin tabbatar da ayyukan na jihar, ya jaddada cewa zai tabbatar da cewa an maido da kudaden da aka karkatar a tsohuwar Gwamnatin Yari. Gwamnan ya ce, "Zan aiwatar da rahoton kwamitin don tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a badakalar. Tun da farko, shugaban kwamitin, Alhaji Ahmed Zabarma, ya fada wa gwamnan cewa kwamitinsa ya gano wasu makudan kudade da aka karkatar yayin gudanar da ayyukan Yari, yana mai kira ga gwamnan da ya kafa kwamitin bincike don karbar kudin. Zabarma ya ce tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, gwamnatin Yari ta ba da kwangiloli 6,180 a wurare daban-daban a cikin jihar "inda da yawa daga cikin kwangilolin ba ayisu yanda yakamata ba ko kum...

Zamukai Gwamnatin Zamfara Kara Kotu: Oshiomhole

Image
Shugaban jam'iyar Apc na Nigeria Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole ya ce jam’iyyar za ta nemi taimakon bangaren shari’a don kawo karshen ayyukan ta’addanci da musgunawa ‘ya’yan jam’iyyar a jihar ta Zamfara. Shugaban j am’iyyar ta APC ya ce dole ne a ba ‘yan jam’iyyar damar gudanar da ayyukansu cikin‘ yanci ba tare da wani nau’i na tursasawa da tsoratarwa daga gwamnatin PDP a jihar Zamfara ko wata jihar da ba su da gwamnoni ba. Oshiomhole ya yi magana ne lokacin da jam’iyyar reshen jihar Zamfara ta gabatar da takarda a gabanta tana zargin gwamnatin jihar da tilasta mambobinta, musamman zababbun shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisa su koma PDP. Oshiomhole ya kara da cewa a cikin dimokiradiyya mai dimbin yawa, dole ne a kyale kowa ya yi amfani da 'yancin walwalarsa. Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta zargi jam’iyyar PDP da jagorantar gwamnati da tirsasawa yayanta komawa PDP dakuma yin barazana ga wadand...