Yakin Taliban
'YAN TALIBAN
(Don Allah a karanta a natse kuma a karanta gaba daya)
Sun rayu a ƙasar Apghanistan Dalilin faruwar wannan Ƙungiya shine:
Bayan ƙasar Russia ta nemi sulhu tsakaninsu da ƙasar Apghanistan akan yaƙin da sukayi shekaru sama goma suna gwazwa wato ƴan mujahid da akafara a 1979-1989 bayan ƙasar ta Rasha batayi nasara ba inda Tattalin Arzikin kasar yayi kusa rushewa inda tayi hasarar manyan kudade makuddai tayi hasarar makamai, toh bayan kasar Saudi Arabia tayi sulhu.
Sai faɗan yakoma tsakanin ƴan ƙasar ta Apghanista suna kisan juna da kansu yazama babu Shugaban ƙasa, babu Gwamna, babu Chairman babu Sarki ko Minista babu wani shugaba a ƙasar kowa yanda yaga dama yakeyi ko Malamai masu bada shawara babu. kasar ta koma In anarchy babu shugabanci kowa ta kansa ya ke mai karfi ya buge marar karfi, babu inda zaka kai kara babu Kotu.
A wannan lokacin sai mutanen ƙasar Russia wadanda kasar ta Apghanistan tayi yaki dasu akayi sulhu suka fara shigowa suna ta'addanci ga 'yan kasar, sai aka samu wani kafiri yace shine Allah mataimakinsa kuma shine Manzon Allah .
A lokacin sai aka kawoma Mullah Muhammad Umar labari lokacin yana karantarwa a wata makaranta, kuma yana karatun Littafin Al-hidaya wato babban littafin Hanafiyya a garinsu wato Kandahar da yake ƙasar ta Apghanistan mashabar Hannafiyya sukeyi.
Sai aka kagayamai kasar nan fa ta lalace babu shugaba babu kowacce irin hukuma ta yaya za'ayi rayuwa haka, gashi kuma an samu wani a bakin garin Kandahar ansamu wasu mutanen ƙasar Russia sunyi check point har shugaban wajen yana cewa shine Allah kuma wasuma suna cewa shine Gwamnan Kandahar.
Akacema Mullah wannan mutun yana tare hanya idan mutun yazo wucewa sai ya tareshi ya karɓe matarsa kuma yayima mutun duka wani lokaci ya kashe mutun suyima matarka fyaɗe idan suka gama su baka matarka ka wuce idan tayi musu sai su karɓeta.
Sai Mullah yace bazai yiyuba mutun yace shi Allah ne kuma yana kisan kai yana yima mata fyaɗe kuma mubarshi Mullah yace tabbas mutashi idan muka gama karatu zamu tashi muje muyi masa wa'azi ya daina idan bai dainaba mu tabbatar da hukuncin Allah akansa.
Bayan sun fita sai sukaje wannan check point ɗin suka samu ana wannan irin case ɗin (wato shi mutunen yana kisan mutane yana fyade wa wasu mata) sai suka buɗe musu wuta suka kashe wasu, wasu suka gudu shidai wanda ke cewa shi Allah ne suka kasheshi.
Daganan suka tashi sunabi anguwa anguwa kwararo kwararo ƙauyuka kauyuka suna wa'azi suna cewa bazai yiyuba ace babu shugabanci kowa takansa yakeyi yakamata asamu shugabanni sai mutane sukace gaskiya yakamata a saurari waɗannan mutanen bai kamata ace babu shugabanci ba.
Kuma a lokacin da Mullah yakeyin wannan ƙokarin yana karantarwa a School of Islamic Science Kandahar
A lokacin duk suna karatu matasan ƴan ainihin Kandahar adadin yawansu Goma sha takwas 18 sunayita Nasiha suna gargaɗi.
Daganan Dattawa sukace yakamata a goyi bayan yaran nan baikamata ace babu jagoranciba ko a ina, sai sukayi yawa sukakai Adadin mutun Ɗari uku da goma sha uku (313) adadin mutanen da sukaje yaƙin Badar kenan.
Sai sukace yakamata mufara fita sauran garu ruwa mucigaba da Nasiha har Allah ya kawo canji. A daina wannan kuncin rayuwa na kisan kai da fasadi.
Alokacin da suka kai hakan a 1-Muharram-1415 24-June-1994 a lokacin suka sakama wannan Ƙungiya suna wato TAHARIQU ISLMAYATIL ƊALIBAN (Saboda la'akari da dokar kowacce kasa ta bada damar ayi kungiya domin kawo zaman lafiya da taimakon al'umma).
A daidai lokacin sai suka nemi gayyatar manya manyan Malaman Ƙasar Apghanistan, a ƙallah Malami Dubu ɗaya da ɗari Uku 1300 suka amsa gayyatarsu. Duk Malaman Ahlul Sunnah dake ƙasar sun gayyacesu saboda sun sani ba'a Addini saida Ilmi da Dattawa. Saboda matashi bazai iya gudanar da rayuwa yanda ya dace ba sai idan akwai wani babba tare da shi, kamar yanda Sayyidina Umar R.A matasa sunada wani tsagi na hauka.
Daga nan ne Taliban ta kafu ainihin Ma'anar Taliban ana nufin Ɗalibai masu neman ilmi a lokacin sai ƙungiyoyin Mujahidun Waɗanda sukayi yaƙi da Russia sai sukace toh sun fahimtci kuma sun gamsu da wadannan 'Yan Taliban din, sai aka haɗa kai.
Ainihin abinda Kungiyar Taliban ta kafu akanshi shi ne: Meaning: of Taliban is a group of students that was Established around 1415 after Hijra in order to establish peace unity low and oder by following the dues and done for then by Shari'a in order to Establish the pious ummah and true orient peoples to submit to the subrenity of their created Allah
Ma'ana: Taliban ƙungiyace ta wasu Ƴan makaranta wacce aka ƙirƙira a shekara Dubu ɗaya ɗari huɗu da goma sha biyar bayan hijra 1415Ah sannan Tana ƙoƙarin samar da zama lafiya da haɗinkai da doka da oda akan tafarkin yanda Shari'a Allah take Sannan su samar da Al'umma mai taƙawa da tabbata kan gaskiya sannan su sallama sallamawa ga Wanda ya halaccisu Allah.
A lokacin sai akace a zaɓi shugaba Malami Dubu Ɗaya da ɗari uku suka zaɓi shugaba (1300) kowa da kowa ya amince babu jayayya babu kace-nace sukace wanda yakamata yazama jagoransu shine MULLAH MUHAMMAD UMAR A lokacin yana ɗan shekara Talatin da ƴan kai.
Sai Alokacin sukace Mullah anzaɓeshine saboda Mutun ne
1. mai kwatanta biyayya ga Allah kuma
2. mutune mai matuƙar ilmi
3. Mai taka tsantsan da Duniya
4. Mutun ne mai damuwa da halin jama'a
5. Yanada biyayya.
6. Jarumta saboda yaƙin da akayi na Russia yana yaro amma ya nuna Jarumta ƙwarai har harbinsa akayi a idonsa na hagu wajen yaƙin (da sukayi wajen kariyar kasar su Apghanistan daga zalunci Rasha) sai likkita yace ya daina alwala yariƙa yin Taimama amma a hakan yake wanke idanuwansa akace ya akayi? yace ya yarda da taimama amma yana ganin wannan harbin kawai bai isa yayi taimamaba.
Bayan Taliban ta fara aiki acikin shekara biyu 07-October-1996 saida yazamo cikin kashi ɗari 100% na ƙasar sunanda wajen Tis'in da ƴan kai 90..%. Duk mafiyawncin mutanen ƙasar sun bisu saboda duk suna ƙoƙari samar da haɗin kai da shugabanci, sai yazama akasar andaina kashe kashen Al'umma sai ƴan kaɗan wasu mutanen da basuda yawa, kasa ta samu zama lafiya, arzikin kasa ya fara dawowa.
Alokacin akasamu Haɗinkai yazama kowa yanada nutsuwa a ƙasar. Ya kasance suka fara gyara makarantun su da aka lalata a lokacin a yakin da sukayi da Russia.
Cikin ikon Allah har lokacin da Mullah Umar wannan abu yasamesu baida Motar hawa takansa ko gidan kansa har ɗakin da yake kwana kamar ɗakin Ɗan Sakandare kuma wataran yaje taro aka bashi Cake yace bayaci sai yazama Apghanistan har walaƙantacce na ƙasar yaci kuma duk yaran da suke biyarsa Ɗalibaine wasu suna University da sauran makarantun ƙasar.
A lokacin sai Taliban suka nemi yakamata yazama sunada halaka da ƙasashen Duniya, amma sai yazama duk Duniya ƙasa uku ce suka yarda da Apghanistan a matsayin gwamnati
1. Saudi Arabia
2. Pakistan
3. UAE Dubai.
Sai sauran ƙasashen arna kamar USA da Russia sukace idan ma zasu yarda sai dai idan Burham deen Rabbaniy ne shugaba, sukace Mulla Umar yayi ƙwacen mulki ne kuma bayan yana kuka aka bashi mulkin yana cewa baya so, duk an tabbatar da hakan cewa baya bukatar shugabanci koda aka bashi.
Sai sukaci gaba da hulɗa da ƙasashe ukun kawai sai suka riƙayi kaɗan kaɗan duk abinda yasaɓama Addini a ƙasar sai su kawar dashi amma babban abinda ke damuwarsu aƙasar shine Gumakan Buddha saboda dama akwai wasu manya manyan gumakan Waɗan da wasu ke zuwa daga wata kasa suna bautarsu alhali kasar babu masu bautar su.
Ɗayan Gumkin yanada tsawon da yakai Mita talatin da biyu 32metres yakai shekara Dubu Ɗaya ɗaya da Ɗari takwas (1800) ƴan Addinin Buddha suka mayar da ƙasar kamar matsayin makkarsu saboda ana bautawa waɗannan gumaka Ɗayan Gumkin yakai tsawon Mita hamsin da ukku 53metres shekararsa Dubu ɗaya da ɗari biyar (1500).
Sai Mullah Umar yace babbar matsala ana shine waɗannan gumakan saboda wasu mutane suna shigowa ƙasarnan da sunan bauta kuma kowa yasan ƙasar Musulmaice.
Sai ƙashashen Duniya na Arna sukace ko nawa su Mullah suke nema za'a basu karsu rusa waɗannan gumakan, Mullah yace muna shiga Kabul abinda zamu farayi shine rusa waɗannan gumakan, saboda yaje yayi zama da Majalisin Malamai Ulama da Minisitas suka zauna ko wanne majalisi masu bada fatawa sukace lokacin da Manzon Allah (S.A.W) yayi Fatahu Makkah meye yafarayi sukace yafara rusa gumaka Ɗari uku da sittin (360).
Sai Mullah yace tunda Manzon Allah (S.A.W) shima rusa gumaka yayi muma hakan zamuyi, akace ko nawa kukeso za'a baku, yace yardar Allah mukeso suna zuwa kawai sai aka rusa gumakan da nakiya.
Daga nan ne Amerika suka saka musu ido sukace sai sun ruguza wannan Ƙungiyar (Taliban).
Dagana Sai Mullah yace Mata su daina yawo babu hijabi kuma maza su tsayar da gemu Malamai ne fiye da dubu suke bada fatawa.
Sukaci gaba da gyaran ƙasa ire iren Jami'oinsu da hanyoyinsu da duk inda yaƙi ya ruguza suna gyarawa kuma sunada matuƙar tarbiyya da Neman Ilmi. Kuma suna taka tsantsan wajen kare rayuwar mutane, basu cutar da mutane.
Daga nan ne Amerika ta fara ƙirƙirar yadda zata tarwatsu daganan sai abidan yafaru a 11-September 2001 Na matsalar harin Pentagon da sauransu daganan sai kawai Amerika tace Usama Bin Laden ne akace shine a nemoshi akashe shi.
Sai Amerika tace Apghanista subasu Usama bin Laden shine yayi wannan aikin sai Mullah Muhammad Umar yace toh idan sunce Usama ne sukawo wani Dalili ko wasu shedanni dazasu tabbatar dashine yayi wannan aika aika.
Sai Mullah yace ko shine yayi bazasu bayar dashi garesuba, saidai suyimai hukunci ko kuwa sukaishi Saudia Arabia saboda bazata yiyuba Musulmi subada Ɗan uwansu Musulmi ba ga Kafirai Saboda Kafiri Azzalumi ne.
Daganan kawai tun ba'a ƙarƙare binciken waye yakai harinba, sai USA tanemi haɗinkan Ƙasashen Duniya, suka fara shirya makamai suka nemi haɗinkan Kashashen Duniya suka samu haɗinkan ƙasa Arba'in (40), Saboda kawai su yaƙi kalilan Ƴan Taliban daganan suka nemi haɗinkan Ƙasar Pakistan suka ajiye Makamansu a kasar ta Pakistan.
Sai Mullah Muhammad Umar yace ku tsaya tukunnan ayi bincike saboda idan kukazo da matsololinku muna sauraronku, bamuda wata matsal da kasarku (Amerika) muna mutunta ku, kar ku kawo muna hari bamu neman kowa da tsokana Addinin Allah mukeyi, sai sukace su babu ruwansu Usama ne kawai ya aikata ku bamushi.
Sai Minister for foreing Affairs na Apghanistan wato: WAKIL AHMAD ALMUTAWAKKIL yace mu bamuda wata matsala daku bamuce zamu yaƙe ku ba amma idan kukace zaku yaƙemu (we are ready to defend our country and our Religion) a shirye muke mukare Ƙasarmu da Addininmu sukace tabbas sai munyaƙeku.
Sai Minister of Defence na ƙasar wato MULLAH UBAIDULLAH yace mufa duk Comandodinmu da Al'ummarmu shirye muke mu kare Ƙasar mu da Addinin mu, saboda kunji muna cewa ayi bincike bawai bamu shirya bane, ah ah kowa a shirye yake fitina ce kawai bamuso munfi son zaman lafiya. Amma idan kunce ah ah to a shirye muke.
Sai Mullah Muhammad Umar Shugaban yace(Amerikan intend to fight the Musulim of Apghanistan) Amerika sunason su yaƙi ƙasar Apghanistan ne da Musulmin ƙasar sai yace ( let Amerika know that war in Apghanista is not a picnic) yace Amerika su sani yaƙi fa ba picinic bane a ƙasar Apganistan yace (if Amerika intend to fight Muslim of Apghanistan or to fight Taliban definitely Taliban is ready to retaliate and America invite for trouble to destroy America and America only) Idan Amerika sun shirya yaƙar Musulmin Apghanistan ko kuma Taliban ba shakka Taliban a shirye take data rama kuma Amerika sun gayyato fitinar da zata tarwatsa Amerika kuma Amerika kaɗai.
Sai Amerika suka fara kai musu hari a 12-october-2001 saida suka daɗe suna Attakin Taliban amma Minista ɗaya kawai suka Illata na Apghanistan.
Amma matsalar anan shine kawai a lokacin Amerika suna kai hari ne ga mutanen gari talakawa waɗanda babu ruwansu sai suje a Islamiyya suyi bombing, akwai wani lokaci da suka kai hari wata Makarantar mata A Kandara sukayi bombing Ɗaliban makarantar hakan yasa Mullah Umar ya kwana yana kuka saboda a ƙallah sun haura mata Dubu ɗaya masu hadda da Malaman duka akayi bombing din su.
Daganan Mullah yace ayi withdraw akoma Daji daganan kafin akoma Daji yaƙi yayi yaƙi har aka kashe ɗan ɗan Mullah Umar wato Yakub Mullah Umar.
Watarana suka turo jirgin yaƙi mai saukar shaho ya sauka har cikin gidan Mullah Umar koda sukazo bayanan yana fagen daga wajen yaƙi saboda ba rago bane.
Aka turo mutun talatin 30 cikinsu su sauko su nemo Mullah Umar sai sojojin Taliban suka halakar da Ashirin da takwas 28 biyu suka sha dakyar saboda basa iya faɗan ƙasa ba saboda su Taliban sunfi iya faɗan ƙasa, dama Musulmi sunfi iya fadan kasa.
Mullah yace kuje mana wajenmu ku same mu ku daina kisan Talakawa saboda sune damuwarmu, sai sukace sai anbasu Usama sai Mullah ya sake kiran mitin na ulama'a, yace mene hukuncin bada Musulmi a hannun kafiri sukace idan akayi la'akari da ƙissar Sulhun hudainiyya da abada Musulmi ɗaya a hannun arna gwara duk Muƙare a Duniya. Saboda lokacin akan Usman ibn Affan Annabi S.A.W yace ayimasa Mubayi'a zaiyi yaƙi koda bai fito da niyyar yaƙiba indai har ankashe Usman mutun fiye da dubu suka yimasa Mubayi'a,
Daganan sukace bai halatta abada Usama ga arnaba, sai Mullah yacema Amerika abisa fatawa ta Ulama baza'a baku Usama ba, saboda haramun ne Amerika sukace ya janye yace shari'a ce fa wallahi bazai kaucema wannan fatawa ba saboda Shari'ar Allah ce.
Daganan sai Mullah yaƙara kiran mitin yace dama ƙoƙarin da sukayi na gina wannan Ƙungiya ta Taliban saboda jinin talakawa dasuke kashe kansu, saboda haka kuma bamason muzama Dalilin kashesu saboda haka mubar gari mukoma a Daji.
Sukayi Dabarar yaƙi suka koma a daji saboda su samu damar mayarwa idan aka yaƙesu.
Kuma dama mafi yawancinsu ƴan kasar 'yan Taliban ne kawai saboda ana gani basu kashe kashen mutane saboda sunada taka tsantsan wajen zubar da jinin Musulmi misali koda ace gawata Mota ta ɗauko wasu manyan makiyan kasarsu amma motar akwai Musulmi ko kuma wani wanda baya yakar kasarsu, koda kuwa baya cikin ƙungiyarsu toh wannan motar zatayi escape baza'a buɗe musu wutaba saboda jinin Musulmi/Ko wanda baya yakarsu ko mutun ɗaya ne kuwa.
A kasar Apghanistan yaki kamar shan ruwan suka dauke shi, wallahi sunada naci wajen yaki musamman ma ace yaki na Akidah ta gaskiya.
A yau Mullah Muhammad Umar baya duniya amma gaskiyar maganar ta bayyana cewa Amerika bata iya hana alkawalin Allah tabbata. Addu'armu Allah yasa wannan sabuwar gwamnati ta 'Yan Taliban ta zama alheri ga Musulmin Apghanistan da duniya gaba daya.
A yau Apghanistan ta zama kasar Musulunci, bayan yakin da akayi shekaru ashirin babu wata biyu ana gwabzawa yau Taliban sunyi nasara.

Comments
Post a Comment