Posts

Showing posts with the label imn

Duk mabiyin El- Zakzaky dan ta'adda ne - 'Yan sanda

Image
Ibrahim El-zazzaky Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce daga yanzu za su dauki duk wani dan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a a matsayin dan ta'adda bisa la'akari da hukuncin babbar kotu da gwamnati ta samu. Sifeto Janar wanda ya bayyana hakan a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja a yayin wani taron manyan 'yan sanda na wata-wata ranar Talata, ya ce ayyukan kungiyar da yunkurin jefa Najeriya rikicin kabilanci. Mohammed Adamu ya yi karin haske dangane da mambobin kungiyar IMN 63 da suka hada da mata bakwai wadanda ke hannun 'yan sandan, inda ya ce daga yanzu duk dan kungiyar ta IMN da suka kama to za su gurfanar da shi ne a gaban kotu domin fuskantar hukunci irin na ta'addanci. Ya kara da cewa " ayyukan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da Sheikh Zakzaky ke jagoranta sun dade suna barazana ga tsaro da doka da oda na Najeirya da kuma zaman lafiya da jogaranci na gari da ma kimar ta...

Shi'a: Gwamnatin Najeriya za ta 'haramta' kungiyar IMN

Image
Aika wannan shafi Facebook   Aika wannan shafi WhatsApp   Aika Image caption Sheikh El-zakzaky ya ce ba zai fasa a bin da yake yi ba Gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'. Jaridar  Punch Newspaper  ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari'ar kasar ne ya nemi hukuncin a ranar Juma'a. Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna 'yan Shi'a." Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya. "Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungi...