Posts

Showing posts with the label izala

Yakamata a yi wa Zakzaky adalci – Sheikh Bala Lau

Image
Bala Lau Shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi wa jagoran 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky adalci. Malamin addinin ya bayyana hakan ne lokacin da yake hudubarsa ta Juma'a a masallacin hedikwatar kungiyar ta JIBWIS da ke Utaku a Abuja ranar Juma'a. Ba wannan ne karon farko ba da wani babban malamin sunnah a kasar yake magana kan batun jagoran 'yan Shi'a a kasar. Sheikh Ahmad Gumi ya taba kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sake shi a baya. Malamin ya ce: "Babu wanda ba ya son a yi wa shugabansu (Zakzaky) adalci. Ko kafiri ne a yi wa adalci. Idan abin da ya yi ba daidai ba ne a hukunta shi saboda gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah." Ya ci gaba da cewa: "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi...