Kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye
Sanata dino melaye Kotun sauraron kararrakin zabe a garin Lokaja na jihar Kogi ta soke zaben Sanata Dino Melaye, wanda yake wakiltar shiyyar Kogi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya. Yayin zaman kotun na ranar Juma'a ne aka soke zaben kuma aka umarci sake sabon zabe a shiyyar. Daya daga cikin mutanen da suka kalubalanci Mista Melaye ne wato Sanata Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ya shigar da kara a gaban kotun. Bayan yanke wannan hukuncin Sanata Melaye ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter. Sanata Melaye ya fara zama dan majalisar wakilan kasar ne a shekarar 2007, inda yake wakiltar mazabar Kabba da Ijumu da ke jihar Kogi. Sai da ya yi wa'adi biyu a majalisar wakilai kafin ya lashe zaben dan majalisar dattawa a shekarar 2015. Kazalika a watan Yuni ne ya bayyana muradinsa na shiga takarar neman gwamnan jihar Kogi, wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.