Duk wanda ya saci yaro a kashe shi - Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar ganduje Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya bai wa ma'aikatar shari'a umarni da ta yi wa dokokin jihar kwaskwarima domin zartar da hukuncin kisa ga masu satar jama'a. Gwamna Ganduje ya ce wannan ce kawai wata hanya da za a iya magance yawaitar salwantar mutanen musamman kananan yara da a baya-bayan nan ake sacewa a fadin jihar ta Kano. A yanzu dai hukuncin masu satar jama'a a jihar shi ne daurin rai da rai. Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake rantsar da kwamitin da jihar ta kafa domin bincike kan hakikanin abin da ya faru dangane da wasu kananan yara guda 9 da rundunar 'yan sandan jihar ta ceto daga jihar Anambra. A makon da ya gaba ne dai rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta ceto yaran guda 9 wadanda ta ce wasu 'yan kudancin kasar' ne suka sace suka kuma sayar da su a jihar Anambra, inda aka sauya musu suna da addini. Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin bai wa yaran da aka ...