Posts

Showing posts with the label borno

Tarihin direban taxi dayazama Gwamna a Nigeria

Image
Gwamnan jihar Borno A ranar Laraba 29 ga watan Mayun 2019 ne aka rantsar da Babagana Umara Zulum a matsayin gwamnan jihar Borno, bayan ya ci zabe karkashin jam'iyyar APC, inda ya gaji Kashim Shettima. Jama'a da dama sun yi shaidar Babagana kan cewa ba mutum ba ne wanda yake son kyalkyalin kayan duniya ko kuma tara makudan kudi, ganin irin damar da ya samu ta tara abin duniya a matakai daban-daban bayan ya sha gwagwarmayar rayuwa. A baya-bayan nan tauraruwar gwamnan na haskawa a Najeriya, inda ake yawan yabon sa da jajircewa da nuna tausayin talaka, musamman halin da mutanen jiharsa ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram. Shin wane ne Babagana Umara Zulum? BBC ta yi nazari kan tarihinsa. Rayuwarsa An haife shi a ranar 26 ga watan Agustan 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a garuruwan Mafa da Monguno tsakanin 1975 zuwa 1985. Tun a lokacin da yake dan aji biyar a sakandare, Babagana ya bayar da himma wajen far...