Posts

Showing posts with the label bello Matawalle

Naira dubu 700 ake biyana fansho - Tsohon gwamna

Image
Balarabe Musa Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ko alawus na musamman na daruruwan miliyoyin naira. Tsohon gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya ce N741,000 ake biyansa fansho a matsayinsa na tsohon gwamna. Ya ce tsoffin gwamnoni a jihar Kaduna, sun amince su karbi fansho daidai da wanda Famanan Sakatare na jiha ke karba. Al'amarin ya ja hankali ne bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya nemi gwamnatin jiharsa ta biya shi naira miliyan 10 a kowane wata a matsayin alawus na musamman, kamar yadda wata dokar jihar ta tanadar. Amma a ranar Talata ne majalisar dokokin jihar ta soke ta, tana mai cewa tsoffin gwamnonin jihar kafin shi sun shafe shekaru ba a biya su kudaden ba a zamanin mulkinsa na shekaru takwas. Wasu masana na ganin cewa bai kamata a ci gaba da biyan tsoffin gwamnoni irin wannan kudin ba, idan aka yi la'akari da matsain tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya. Masana irinsu Farfesa Jibr...

Dalilin cire sakataroran dindindin 21 a Zamfara

Image
Gwamna Bello Matawalle Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce ya yanke shawarar sauke wasu sakatarori 21 na dindindin saboda sun gaza cin jarabawar cancanta da gwamnatin jihar ta gudanar. Mai ba da rahoto ga manema labarai a Gidan Gwamnati, Gusau, yace ranar Juma'a, Matawalle ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawarar rage yawan sakataroran dindindin saboda jihar tana da sakataroran dindin mafiyawa a Arewa Maso Yamma. Ya ce, “Duk abubuwan da aka tantance sun nuna cewa jiharmu tana da manyan sakatarorin dindindin fiye da kowace haha a Arewa maso Yamma, kuma mun kafa kwamiti na sake fasalin don tabbatar da cancantarsu. Saboda haka kwamitin ya gayyaci dukkan sakatarorin dindindin da kuma wasu mutane shida wadanda gwamnatocin da suka shude suka sauya mukamansu suka gabatar da su a rubuce da kuma tattaunawa don tantance su. "Ya danganta da sakamakon tantancewar, mutum 26 ne kawai suka cancanci riĆ™e matsayin sakatarorin na dindindin." Gwamnan ya y...

Tatattun bayanan Firar da akayi da Gwamnan Zamfara

Image
Gwamna Matawalle Yafara da yiwa al'ummar jihar Zamfara godiya akan wadannan nasarori da Gwamnatinsa ke samu ya bayyana wannan nasara dacewa addu,ar da Yan Zamfara suka Dade sunayi ce takawo wannan nasara. Yakuma bayyana sulhun da suka da Yan bindiga Sulhu ne fasukayi tsakani da Allah Babu yaudara aciki kuma za'a samu tabbataccen Zama lfy Mai dorewa a jihar Zamfara. Yakumace bayan zuwansa Kanoma ansamu matsaloli dasuka Kai har akadakatar da Sarkin Maru. Bayan wannan yaje yasamu Shugaban kasa Buhari yabashi bayanai akan yanda matsalar tsaro jihar Zamfara take, kuma Shugaban kasa yaji dadi da zuwansa yakuma yimasa alkawarin yimasa duk abinda yakeso Domin Zamfara ta zauna lafiya, sannan Shugaban kasa yabada taimakon buhun taki duhu dari da arba'in da takwas da dari biyar 148,500, kuma Shugaban kasa yabada dama ayi binciki aga irin barnar da akayi azamfara Domin aginama wasu da wannan matsala ta shafa gidaje. Yakumace Fita ta ta farko da yayi zuwa saudiyya don in go...