Tatattun bayanan Firar da akayi da Gwamnan Zamfara
![]() |
| Gwamna Matawalle |
Yakuma bayyana sulhun da suka da Yan bindiga Sulhu ne fasukayi tsakani da Allah Babu yaudara aciki kuma za'a samu tabbataccen Zama lfy Mai dorewa a jihar Zamfara.
Yakumace bayan zuwansa Kanoma ansamu matsaloli dasuka Kai har akadakatar da Sarkin Maru. Bayan wannan yaje yasamu Shugaban kasa Buhari yabashi bayanai akan yanda matsalar tsaro jihar Zamfara take, kuma Shugaban kasa yaji dadi da zuwansa yakuma yimasa alkawarin yimasa duk abinda yakeso Domin Zamfara ta zauna lafiya, sannan Shugaban kasa yabada taimakon buhun taki duhu dari da arba'in da takwas da dari biyar 148,500, kuma Shugaban kasa yabada dama ayi binciki aga irin barnar da akayi azamfara Domin aginama wasu da wannan matsala ta shafa gidaje.
Yakumace Fita ta ta farko da yayi zuwa saudiyya don in gode ma Allah akan nasarar da ya ba ni.
Sanna akwai wani Dan asalin jihar Zamfara da gwamnatin saudiya ke tsare dashi shekara biyu da rabi sbda ansamasa kwayoyi cikin kayansa, nanemi da asakoshi yanzu haka Shugaban kasa ake jira yasa hannu asakoshi.
Fita ta ta biyu 2 kuma ya tafi abuja ne sanadiyyar wata rana suna tattaunawa tare da ma su garkuwa da mutane, sai anka kira daya daga cikin su cewa ga sojoji cen na bude wuta a wuraren zaman su, sai yacce man shi ko ko zaman sulhun nan yaudara ce ?
An gayyato mu ayi sulhu amma kuma ga sojoji chan na nude ma mutanen mu wuta.
Yakuma ce da safiyatayyi sai ya tafi Abuja wajen brutai, shugaban sojan sama, IG police inda na roke su da a tsagaita bude wuta saboda tattaunawa sulhu da mu ke yi.
Yakumace akwai hukumomin kasar Qatar da sunka yi alkawalin samar da masallatai 15 da kuma fanfunan tuka- tuka
Yakumace Na nemo kamfani da za su kashe dala biliyan daya $1b inda za a tada masakun zamfara da su, gyara kwangirin jirgi, habbaka hakar ma'adinai da gina filin jirgin sama kuma za Samar da wutar lantarki daga Bakalori Dam dazata bada jihar Zamfara da sauran jihohin arewa sannan kuma wadan nan kudaden ba bashi ba ne.
Sannan kananan, hukumomin Maradun, Anka, mada, birnin magaji za su amfana da tallafin magunguna na hukumar sojin sama ta nijeria inda yanzu haka tauwagar wadan nan sojojin tuni ta na cikin jahar zamfara.
Yakumace Na tura mataimakina domin nemo babbar na'urar rarraba wuta (transformer) mai nauyin kilo 60 kuma an samu sannan a cikin satin nan za a kawo ta a jahar zamfara domin taimakawa wajen bunkasa samarda wutar lantarki.
Yakuma ce a bangaren harkar Ilmi TETFUND ta ba mu $1bn kuma ba da jimawa ba za a fara aikin gyaran makarantar Abdu Gusau Polytechnic.
Yanzu haka mun tsara fitar da ba da kwangilolin gina sabbin azuzuwa 613, gyara azuzuwa (renovation) guda 342, VIPs 2 akwai kujerin Zama na yara guda 14,810 dakuma kujerin Zama na malamai guda 962 dakuma ICT center guda goma Sha biyu 12.
Sannan kuma yace ban yarda a fita wajen jahar zamfara a sayo kayan da za a aikin kwangila ba.
Ban yarda a fita wajen jahar zamfara a dauko ma'aikatan da za su ayukkan kwangila a zamfara ba.
Zan sa hukumar ZAROTA ta kama kayan da anka shigo da su daga wajen jahar zamfara.
Sannan duk dan kwangilar da anka samu yana sawo kayan kwangila daga wajen jahar zamfara, wallahi ba zan kara ba shi kwangila ba.
Duk mutanen da munka karbo daga ma su garkuwa da su, wallahi ba mu taba baiwa kowa ko sisin kobo ba. Sannan akwai Mutanen tsohuwar Gwamnati masu zuwa suna cema Mutanen da akayi Sulhu dasu bada gaske akeyiba karsu yarda, wayan Nan Mutanen bamasu son al'ummar jihar Zamfara bane.
Sanna yace duk wanda gwamnati ta karbe ma fili ba'a biyashiba a yankin tsaune ya koma ma filin shi indai akan zalunci gwamnatin da ta gabata ta karbe shi.
Sannan yace Sakatarin gwamnatin a tabbatar da albashin wannan watan ya tafi tare da kuddin hutun ma'aikata domin ma'aikata su samu sukunin sayen raguna.
Sannan kuma Sakatarin gwamnati a tabbatar da an bincika kuma an kama duk mai hannu a cikin zabtaren albashin ma'aikata babu gaira babu dalili kuma yanzu haka akwai yaron tsohon gwamna da yanzu haka akwai irin wadan nan kudade har da na pension da sunka kai #3bn kuma wallahi sai ya kawo su.
Sann Akwai shirin tallafa ma matasa 8,000 inda za a dinga tallafa ma su da kudade duk wata.
Kuma Za a dinga daukar macce 1,800 kowane wata ana ba su tallafin #20,000 kowane wata inda za a dinga chacchanzawa kowane wata kuma yanzu haka na ba da na wata biyar kasa.
Nakuma samo ma dalibi 200 admission kuma gar a karbi kuddin kowane dalibi, na ba da miliyan 5 ayi ma kowane dalibi passport kuma gwamnati za ta dauki nauyin biyan kuddin jirgin su.
Sannan kuma Gwamnatin tarayya ta aminta da kamfanin taki na jahar a matsayin dai daga cikin kamfanonan da za su dinga buga takin gwamnatin tarayya sabanin a chan baya inda sai dai ayi haka a huntuwa
Na baiwa kamfanin taki na jahar zamfara #10m kuma na sake na ba su #50m domin su sawo kayan aiki (raw materials).
Yanzu nan ake turo man da sako cewa an sako wani dan kabikar Igbo a yankin dansadau wanda yanzu haka yana fadar gwamnati.
A cikin yan tauwagar shi akwai :
1. Mataimakin sa Barrister Mahdi Aliyu Gusau
2. Mai girma sakatarin gwamnatin jahar zamfara, Alh. Bala Bello Maru (Sarkin Kudun Maru)
3. Abubakar Justice DAURAN
4. Bashir MAISHINKAFA
Allah ya taimaki wannan Gwamnati da manufofinta na alkhairi yakuma taimaki jihar Zamfara yakuma Kara bamu zaman lafiya Mai dorewa Ameen.
Suleiman Muhammad Maradun

Comments
Post a Comment