Posts

Showing posts with the label tabawa balewa

Matar Margayi tafawa balewa tarasu

Image
Margayi tafawa balewa da matarsa Hajiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa wacce ita ce matar da ta rage ga Fira Ministan Nijeriya na farko, Marigayi Abubakar Tafawa Balewa ta rigamu gidan gaskiya a Lahadin 27 ga watan October 2019. Majiya daga iyalai sun bayyana cewa da yammacin ranar Lahadi ne Hajiya Jummai ta rasu a wani asibiti da ke jihar Legas. Sun bayyana  cewa, kwanan baya an kai marigayiyar asibiti a kasar Indiya domin nema mata kulawar likitoci kana an sallameta daga asibitin a makon jiya, inda ta dawo Nijeriya don ci gaba da jinya. Majiya daga makusantan ya kuma kara da cewa matar jarumin Nijeriyan ta dawo Nijeriya inda ta tsaya a Legas domin hutawa daga bisani ta karaso jihar Bauchi domin ci gaba da kula da lafiyarta, “Abun bakin ciki, da safiyar yau Lahadi rashin lafiyar nata ya sake tashi inda har ta kai ga ta suma, daga bisani Allah ya dauki rayuwarta,” A cewar majaliyar. Ana sa ran cewar za a dawo da ita jihar Bauchi a ranar Litinin domin jana’iza da kaita...