Posts

Showing posts from May, 2019

Cikakken Tarihin Bello Matawalle

Image
Zabebben Gwamnan Zamfara Gwamnan jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed Matawallen Maradun shahararen dan siyasa ne daya shahara  amatakin jaha dakuma tarayya, yashafe shekaru 20 ana gwagwarmaya dashi a harkar siyasa. Bello Matawalle dan kimanin shekara 49 mahaifinsa yarasu tun yana karami yatashine tare da mahaifiyarsa, Su biyar ne a wajen mahaifiyarsu da mahaifinsu Mata 2 Maza 3. an haifeshi a karamar hukumar  mulki ta Maradun 12 ga December 1969, yayi karatun primary a Maradun yakammala a 1979 yayi Secondary dinsa a jihar kebbi a karamar huukumar Bunza ya kammala a shekarar 1985  yakuma je Yaba College of Technology lagos dakuma Thames valley university a London. Yayi Commissioner a ma'aikatar lafiya a tsohuwar jihar Sokoto, daga bisani yazama malamin makaranta a colleging Mata dake Moriki da Kwatarkwashi, daga bisani kuma yakoma aiki a ma'aikatar Ruwa ta  birnin tarayya Abuja. Bello Matawalle yashiga harkokin siyasa ne a 1998 a karkashin jam'iyar united Nig...

Buhari ya sa hannu kan kasafin kudin 2019

Image
Shugaba Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.91. A watan Disambar 2018 ne dai Shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar dokokin kasar kasafin na naira tiriliyan 8.83. To sai dai majalisar ta kara naira biliyan 90 da miliyan 300 inda ta amince da kasafin na naira tiriliyan 8.91. An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana. Har wa yau, an gina kasafin bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan kowace ganga, da kuma kan farashin canji N305 kan dala daya. Idan za a iya tunawa dai Shugaba Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019. Shugaban ya ce wannan shi ne jawabin gabatar da kasafin kudi na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas. Wannan ne kuma kasafi na karshe da shugaban ya gabatar a wa'adin mulkinsa na farko da ke karewa ranar Laraba. A jawab...

Zaben da muka yi mun yi kura-kurai - Gwamna Yari

Image
Gwamnan Zamfara mai Barin Gado Gwamnan Zamfara mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da hukuncin kotun koli tare da yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri. A yayin da yake jagorantar shan ruwan azumin ramadan na karshe tare da kwamishinoni da manyan kushoshin gwamnatinsa a gidansa da ke Talatar Mafara gwamnan ya ce "mun aminta kuma mun yadda da hukuncin Ubangiji." A ranar juma'a ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fitar da gwani ba wanda hakan ya yi sanadin soke kuri'un da jam'iyyar ta samu a dukkanin kujerun da ta lashe a zaben 2019 a jihar. Hukumar INEC kuma ta tabbatar da 'yan takarar jam'iyyar PDP da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben na gwamna da na 'yan majalisar Tarayya da na jiha. Da yake jawabi, Gwamna Yari ya amsa cewa zaben da aka yi akwai kura-kurai a ciki, inda ya ce sun yadda da hukuncin kotun koli, "wannan tsari ne wanda Allah ya riga ya tsara haka....
Image
Although he came second in the March governorship election in Zamfara, Bello Matawalle has been a key political player both at the federal and state levels for several years. The 49-year-old Peoples Democratic Party candidate has been in the political space for at least 20 years, serving as commissioner and member of the House of Representatives. The March 9 governorship election was his first shot at becoming a governor. He lost out after the Independent National Electoral Commission (INEC) permitted the All Progressives Congress (APC) to field a candidate barely 24 hours to the day of the election. The electoral body declared the APC candidate, Muktar Idris, winner of the polls. The collation officer, Kabiru Bala, a professor at the Ahmadu Bello University, Zaria, said the APC candidate polled 534,541 to defeat Mr Matawalle who got a distant 189,452. Mr Matawalle rejected the result and vowed to “reclaim his stolen mandate” at the elections petitions tribunal. ...

Zan magance matsalar tsaro a jihar Zamfara - Bello Matawalle

Image
Zababben Gwamnan jihar Zamfara Bayan tabbatar masa da nasara, gwamnan jihar Zamfara mai jiran gado, Muhammad Bello Matawalle ya ce rashin adalci na daga manyan dalilan da suka haifar da rashin tsaro a jihar Zamfara. Sabon gwamnan wanda tsohon shugaban kwamitin tsaro ne na majalisar wakilai ta Najeriya, ya ce kwarewarsa ta sa ya fahimci hanyoyin da zai bi wajen kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da ita. A ranar Asabar ne hukumar zabe ta Najeriya INEC ta bayyana Bello Matawalle na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan Zamfara. Shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja inda ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ita ce ta yi nasara a dukkanin guraben jihar sai dai an samu gurbi daya na majalisar jiha inda dan jam'iyyar NRM wato Kabiru Hashimu ya lashe kujerar mazabar Maru ta kudu. Ya ce wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma'a inda ta soke guraben dukkanin 'yan takarar jam'iyy...

Ya kamata ministocina su yi alfahari da kansu – Buhari

Image
Shugaba Buhari da Ministocinsa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa ministocinsa cewa ya kamata su yi alfahari da kasancewarsu wani bangare na "gwamnati mafi sanin makama". Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron majalisar ministoci ranar da ake yi duk ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja. Wannan dai shi ne zaman da shugaban ya yi a majalisar zartarwarsa na karshe da ministocinsa. Sai dai shugaban ya ba su damar ci gaba da aiki har zuwa 28 ga watan Mayu, inda za su mika takardar ajiye aiki ga sakataren gwamnati Boss Mustapha, kwana daya kafin a rantsar da sabuwar gwamnatinsa a mako mai zuwa. Da yake jawabi a cikin dakin taron, Shugaba Buhari ya ce sunayen ministocin ya shiga cikin tarihin Najeriya, wanda hakan abin alfahari ne. "Kowannenku yana da wata baiwa ta musamman kuma mu ne hoton Najeriya da muke fatan ginawa. Kasa mai kabilu da dama wadda kowanne dan kasa yake da 'yancin fadar albarkacin bakinsa. "Ya kamata ku yi alfahari da k...

Abin da ya sa mutane suka yi zanga-zanga a Katsina

Image
Gwaman Mutane Kura ta lafa a garin Batsari na jihar Katsina, bayan arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke nuna rashin jin dadinsu da tabarbarewar halin tsaro a jihar. Masu zanga-zangar sun fusata ne da kisan mutane fiye da 13 a wani kauye da ke kusa da garin, kuma daga cikin wadanda aka kashe akwai yara kanana. Wasu rahotanni sun ce an kuma kai hare-hare a yankunan Dan Musa da Faskari. Wani mazauni Batsari ya ce 'yan bindiga sun bude wuta ne kan mutanen da suka fita gona yin shuka da safiyar ranar Talata. Ya ce hatsaniyar da aka samu ta tashi ne bayan da mazauna kauyen da ake kira 'Yar Gamji suka kwaso gawawwakin mutanen suka jibge a kofar gidan mai garin Batsari. "Dama akwai dubban 'yan gudun hijira a garin, shi ya sanya mutane suka fito zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan matsalar tsaro," in ji shi. Ya kuma ce masu zanga-zangar suna cewa ne a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen kashe-kashen rayukan mutane da ake yi ku...

'Yan sanda Sunyi arangama damasu Zangazangaa Katsina

Image
Gwaman Mutane Masu Zanga Zanga Kura ta lafa a garin Batsari na jihar Katsina, bayan arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke nuna rashin jin dadinsu da tabarbarewar halin tsaro a jihar. Masu zanga-zangar sun fusata ne da kisan mutane fiye da 13 a wani kauye da ke kusa da garin, kuma daga cikin wadanda aka kashe akwai yara kanana. Wasu rahotanni sun ce an kuma kai hare-hare a yankunan Dan Musa da Faskari. Wani mazauni Batsari ya ce 'yan bindiga sun bude wuta ne kan mutanen da suka fita gona yin shuka da safiyar ranar Talata. Ya ce hatsaniyar da aka samu ta tashi ne bayan da mazauna kauyen da ake kira 'Yar Gamji suka kwaso gawawwakin mutanen suka jibge a kofar gidan mai garin Batsari. "Dama akwai dubban 'yan gudun hijira a garin, shi ya sanya mutane suka fito zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan matsalar tsaro," in ji shi. Ya kuma ce masu zanga-zangar suna cewa ne a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen kashe-kashen rayukan mu...

Laifin gwamnati ne matsalar tsaro a Najeriya- PDP

Image
Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce matsalolin da al'ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya sa rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki. Sanata Umaru Tsauri, sakataran kasa na jam'iyyar PDP ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC. Ya ce rashin fadar gaskiyar lamurra game da halin da kasa ke ciki daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka jefa kasar cikin halin rashin tsaron da take ciki. An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan sa-kai da masu satar mutane Birtaniya za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta'addanci Ba mu gaza ba wajen yaki da masu satar mutane - Dambazau Ya ce "babu abin da ya jawo wannan matsala illa gwamnati ta ki yarda ta fadi wa mutane gaskiya cewa wannan abu na faruwa, kuma a dauki mataki." Ya kuma ce aikin gwamnati ne ta gano wadanda ke da hannu cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar tsaro a Najeriya, ba jama'ar kasar ba. Sanata Umaru Tsauri ya ce halin da Najeriya ...

Mun gama da masu satar mutane – Sufeton 'Yan Sandan Najeriya

Image
Sufeton 'Yan sandan Nigeria Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce jami'an tsaro sun ci galaba a kan masu satar mutane don neman kudin fansa a kasar. Sai dai ya ce akwai sauran aiki a gaba "don ba wai gaba daya muka gama da su ba. Amma mun ci galaba a kansu sosai-sosai." Babban sufeton ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kawo karshen matsalar satar mutune a kasar. Ya bayyana hakan ne lokacin wani taro na shugabannin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da ke yankin Afirka ta yamma (WAPCCO) a makon jiya. Kazalika ya musanta batun da wasu masu sharhi suke cewa tsaron cikin gidan kasar ya gagari 'yan sanda. "Sojoji suna aiki da 'yan sanda ne don su taimaka, amma duk inda ka tafi a duniya idan dai maganar tsaro na cikin gida ne 'yan sanda ne ke kan gaba." Ya ce dukkansu suna yi wa gwamnati ne aiki, "kuma abin da dan Najeriya ke so shi ne zaman lafiya." "Aiki ba wai ya gagari 'ya...

Kunsan ya jikinku kan kasance a lokacin Azumi

Image
A kowacce shekara miliyoyin musulmai suna azumi tun daga fitowar rana har faduwarta, na tsawon kwanaki 20 ko 30 a cikin watan Ramadan. A shekarun baya-bayan nan dai Ramadan na fadowa ne a watannin bazara a kusurwar duniya daga arewa, hakan zai janyo ranaku masu tsawo da kuma yanayi mai dumi. Hakan na nufin cewa wasu kasashe kamar su Norway, mutane za su yi azumi na tsawon sa'o'i 20 a wannan shekarar. Shin yin azumi zai iya yi wa jikin mutum illa? Ga abin da ke faruwa da jikinku idan kuka yi azumi na tsawon kwanaki 30. Lokaci mafi wuya - kwanaki biyu na farkon azumi A ka'ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa'a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci. Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin. Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi. Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai k...

Kasar da zubar da ciki ya fi haihuwa yawa

Image
Jariran Yara Piia mazauniyar kasar Greenland ce, mai shekaru 19 inda ta shaida wa BBC cewa ''mu a kasarmu ba ma tababa wajen maganar zubar da ciki, muna yi ne a bayyane, na tuna lokacin da nake ba kawayena da 'yan uwana labarin lokacin da na taba yi.'' Ta zubar da ciki sau biyar a shekaru biyu Matsashiyar ta bayyana cewa ''ina amfani da kariya domin hana daukar ciki, amma wani lokaci ina mantawa. A halin yanzu ba zan iya haihuwa ba, sakamakon ina shekarar karshe a makaranta.'' Tun 2013, an samu kusan haihuwa 700 da kuma zubar da ciki 800 a duk shekara kamar yadda kiddidigar gwamnati ta bayyana. Amma me ya sa ake yawan zubar da ciki a kasar Greenland? Karancin tsangwama Greenland ita ce kasa mafi girma da ke kan tsibiri me yawan mutanen da ba su wuce 55,000 ba kamar yadda kasar ta fitar da kididdigar yawan mutanenta a 2019. Sama da rabin matan da ke daukar ciki a kasar na zubar da cikinsu. Wannan na nufin a kasar mata 30 cikin 1...

Yadda za ku kauce fadawa rikici da 'yan sandan Najeriya a kan hanya

Image
Yin murmushi da da'a da kuma gudun yin fada da dan sanda na cikin abubuwan da ke taimakawa direba a duk lokacin da ya zo gaban shingen bincike na 'yan sanda kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter. Ba a bayyana takamaiman dalilin da ya sa rundunar 'yan sandan ta wallafa wadannan shawarwarin amma ana ganin an wallafa ne sakamakon wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta na wani dan sanda na da ke cin mutuncin wani direba. A cikin bidiyon, an nuna wani dan sanda inda ya bukaci a ba shi cin hancin naira 4,000 saboda abin da direban ya yi niyyar ya ba shi bai kai hakan ba. Irin wadannan lamuran sun sha jawo a harbe direbobi su mutu sakamakon kin bayar da kai bori ya hau. 'Yan sandan ba su yi magana a kan karbar cin hanci ba, amma a shawarwarin da suka bayar na mu'amala cikin mutunci da 'yan sanda a yayin da aka same su a gaban shingen bincike na kanya sun bayar da shawarar cewa: ''A lura da suna ko lamba ko kuma motar jami'...

Ko Gwamna Ganduje zai jingine nadin sabbin sarakuna?

Image
Gwamna Ganduje na Kano Kwamishinan shari'ah na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtari ya fada wa BBC cewa har zuwa daren ranar Juma'a, bai karbi wani umarni daga kotu (game da batun nada sabbin sarakuna da kirkirar karin masarautu na gwamnatin Kano) ba. Babbar kotun jihar Kano ce ta ba da umarnin cewa gwamnati da majalisar dokokin jihar su dakatar da duk wani mataki na kirkirar sabbin masarautu a jihar ta Kano har sai ta saurari karar da wasu 'yan majalisa suka shigar gabanta suna kalubalantar matakin yin dokar. "Ban san da kara ba, kawai dai yadda kuke ji a gari, (ni ma) haka nake ji a gari." Barista Ibrahim Mukhtari ya ce: "Ni ban ga oda ta kotu ba kowacce iri." Ya kara da cewa don haka ba za su ce komai a kai ba, har sai sun ga takardar kotu. Za dai a zuba ido a gani ko gwamnatin jihar Kano za ta dakatar da nadin sarakunan a ranar Asabar kamar yadda ta tsara bisa umarnin kotu, ko kuma za ta yi biris da umarnin ta ci gaba da shagulgulan bai ...

Manyan Malaman Kano: Abin da ya sa muka bar gwamnatin Ganduje

Image
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Wasu manyan malaman addinin musulunci a Kano da suka hada da Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Shaikh Abba Adam Koki, shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano da Dr Muhammad Nazifi Inuwa da kuma Malam Abubakar Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje. Wata sanarwa da malaman suka sanya wa hannun ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda ayyukan da suke gabansu. Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da shi ta waya, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun fita daga gwannatin ne saboda sun ga ba a bukatar aikinsu. Shi kuwa a cikin takardar da ya mika ta murabus dinsa Shaikh Abba Adam Koki ya ce ya ajiye aikin ne saboda dalilan rashin lafiya. Shaikh Daurawa dai shi ne babban kwamandan Hisbah ta jihar Kano, shi kuma Shaikh Abba Koki shi ne shugaban hukumar alhazai ta jihar. Malam Nazifi Inuwa ya rike mukamin kwamishina na biyu a hukumar Zakka ta jihar Kano, yayin da shi kuma Malam Abubakar Kandahar ya rike mukamin k...

Kungiyoyin Ingila sunkafa tarihi a Turai

Image
'Yan wansan manyan kungiyoyi Kungiyiyoin Ingila sun kafa tarihi a harkar kwallon kafar Turai bayan da hudu daga cikinsu suka kai wasan karshe a manyan gasar nahiyar. Arsenal ta ci wasanta a Valencia yayin da ita kuma Chelsea ta doke Eintracht Frankfurt a ranar Alhamis, inda suka kai wasan karshe a gasar Europa League. Kafin haka an yi karon-batta tsakanin Liverpool da Barcelona da kuma Tottenham da Ajax a gasar Champions League. Wannan ne karon farko da aka samu kungiyoyi hudu daga kasa daya da suka kai wasan karshe a gasar biyu. An taba samun 'yan Ingila da suka buga wasan karshe a gasar Europa ta 1971-1972, sai kuma a Champions League, inda Man United ta doke Chelsea a bugun fenareti a shekarar 2007-2008. 'Yan Spaniya sun biyu sun buga wasan karshe a Champions League ta 2015-2016, inda Real Madrid ta doke Atletico Madrid yayin da kuma kungiyar Sevilla ta ci kofin Europa League a shekarar. "Gasar Premier Ingila mai zafi ce sosai kuma ita ce kan gaba...

Ramadan: Tsawon lokutan azumi a kasashen duniya

Image
Add caption Watan Ramadan na cikin watanni mafi tsarki ga Musulmin duniya, kuma lokaci ne da suke kara dukufa wajen yin ibada da ta hada da salloli cikin dare da azumi a tsawon kowane yini na watan. Kasashen da ke yankin tsakiyar duniya da aka fi sani da 'equator'da turancin Ingilishi sun fi samun gajeren lokaci, amma Musulmin da ke kasashen da ke arewacin duniya na dadewa kafin rana ta fadi saboda tsawon yini da ake fuskanta a lokutan zafi. Ku latsa kasa don ganin yadda abun yake: Afghanistan Tsawon lokacin azumi: Sa'a 15 da minti 4 Fajr: 03:39 Fitowar rana: 04:57 Faduwar rana: 18:43 Afirka ta Kudu Tsawon lokacin azumi: Sa'a 12 da minti 3 Fajr: 05:30 Fitowar rana: 06:35 Faduwar rana: 17:33 Amurka Tsawon lokacin azumi: Sa'a 15 da minti 2 Fajr: 04:40 Fitowar rana: 05:57 Faduwar rana: 19:42 Australia Tsawon lokacin azumi: Sa'a 11 da minti 44 Fajr: 05:24 Fitowar rana: 06:35 Faduwar rana: 17:08 Birtaniya Tsawon lokacin azumi: Sa'...

Kalaman Buhari kan tsaro sun jawo ce-ce-ku-ce

Image
Sufeton 'Yan sanda, Shugaba Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban sufeton 'yan sanda kasar na kokari matuka wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar. Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo kasar bayan kwashe kwanaki 10 a birnin Landan. Shugaban ya ce "ga duk wanda ya san sufeton 'yan sanda to zai fuskanci ya rame sosai saboda tsabar aikin da yake yi." Hakazalika a lokacin da dan jaridar tashar talabijin din kasar NTA ya yi masa tambaya kan kafa sabuwar gwamnati, Buhari ya amsa da cewa "ba zan ce komai a kai ba." Sai dai wadannan kalaman nan shugaban sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kasar. Wasu suna ganin bai kamata shugaban ya yi su ba, ganin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a kasar da kuma yadda ake satar mutane don neman kudin fansa ba dare, ba rana a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna. Cikin kwanaki da shugaban ya shafe baya kasar an samu matsaloli tsaro da dama da garkuwa ...

'Yan Najeriya na kewar 'Yar Adua bayan Shekara 9 da mutuwarsa

Image
Margayi Ummaru Musa 'Yar adua Jama'a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da ta'aziyyar rasuwar shugaban kusan shekaru 9 kenan bayan rasuwarsa. Jama'a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi kan wasu abubuwan alheri da ya shuka a lokacin mulkinsa da suka hada da rage kudin man fetur, karin albashi musamman ga 'yan sanda. Haka ma dai ana ci gaba da tunawa da shi wajen irin rawar da ya taka wajen ganin cewa an samu sulhu da tsagerun yankin Niger Delta a wancan lokaci inda ya samar masu da sana'o'i da tallafin karatu da dai sauransu. Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ba a bar shi a baya ba wajen tunawa da Marigayi 'Yar'adua domin a shafinsa na Twitter ya tuna da irin ayyukan da ya gudanar na gina kasar a wancan lokaci. Rasuwar Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya. Kafin rasuwarsa, ya...

''Yan fashi sun kashe sama da mutum 30 a Zamfara'

Image
Hanyar Dan Sadau a Zamfara Sarkin Kudun Dan Sadau a jihar Zamfara ya shaida wa BBC cewa 'yan fashin daji sun kashe sama da mutum 30 lokacin da suka auka wa kauyen Dan-Gurgu na masarautarsa tare da jikkata karin wasu 12. Alhaji Hussaini Umar ya ce dukkan mutanen da abin shafa maza ne, wadanda aka far wa a lokacin da suke haramar tafiya gonakinsu wayewar garin ranar Asabar. Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammed Shehu ya ce mutum goma aka kashe yayin wannan hari, tare da jikkata karin wasu hudu. Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan fashin daji, wadanda kan far wa kauyuka, su kashe mutane, tare da kona gidajensu har ma da dukiyar da suka mallaka. Ko da yake da farko sun fara ne da satar mutane, inda sukan rike su har sai dangi ko makusantansu sun biya kudin fansa. Masarautar Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru ta yi makwabtaka da yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, wanda ya yi kaurin suna ...