Cikakken Tarihin Bello Matawalle

Zabebben Gwamnan Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed Matawallen Maradun shahararen dan siyasa ne daya shahara  amatakin jaha dakuma tarayya, yashafe shekaru 20 ana gwagwarmaya dashi a harkar siyasa. Bello Matawalle dan kimanin shekara 49 mahaifinsa yarasu tun yana karami yatashine tare da mahaifiyarsa, Su biyar ne a wajen mahaifiyarsu da mahaifinsu Mata 2 Maza 3. an haifeshi a karamar hukumar  mulki ta Maradun 12 ga December 1969, yayi karatun primary a Maradun yakammala a 1979 yayi Secondary dinsa a jihar kebbi a karamar huukumar Bunza ya kammala a shekarar 1985  yakuma je Yaba College of Technology lagos dakuma Thames valley university a London.

Yayi Commissioner a ma'aikatar lafiya a tsohuwar jihar Sokoto, daga bisani yazama malamin makaranta a colleging Mata dake Moriki da Kwatarkwashi, daga bisani kuma yakoma aiki a ma'aikatar Ruwa ta  birnin tarayya Abuja.

Bello Matawalle yashiga harkokin siyasa ne a 1998 a karkashin jam'iyar united Nigerian congress party (UNCP). Yakuma tsaya takarar Chairman na karamar hukumar mulki ta  Maradun a 1999 a karkashin Jam'iyar APP amma abokin takararsa na wancen lokaci Ibrahim dan Malikin gidan goga na Jam'iyar PDP yayi nasara akanshi, daga bisani Gwamna maici a wancen lokacin Ahmad Sani yariman Bakura yayimasa Commissioner a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, dakuma ma'aikatar cigaban birane, dakuma ma'aikatar matasa da wasanni a tsakanin shekarun  1999 zuwa 2003.

Yazama zababben dan Majalisar tarayya mai wakiltar Bakura da Maradun a 2003 da 2007 a jam'iyar APP  da ANPP. a 2011 ya cenza jam'iya daga ANPP zuwa PDP yakuma kara zama dan majalisar tarayya, a wancen lokacin shikadai ne dan majalisar daya tsayama jam'iyar PDP takara a jahar Zamfara kuma yayi nasara, a 2015 yanemi takarar dan majalisar dattijai mai wakiltar Zamfara ta yamma amma abokin takararsa tsohon mai gidansa na jam'iyar APC Ahmad Sani Yariman Bakura yayi nasara akanshi. Yarika mukamai a majilasa kamar haka mataimakin shugaban marasa rinjaye, shugaban marasa rinjaye, dakuma shugaban commiting tsaro da asiri na majalisar tarayya a shekarun 2003, 2007, da 2011.

A 2019 yazama dan takarar Gwamna a karkashin jam'iyar PDP yakuma zo nabiyu a babban zaben da aka gudanar a watan maris. Yazama zababben Gwamna ne bayan rikin siyasar daya dabaibaye jam'iyar APC wanda wasu yayanta suke kalubantar cewa batayi Zaben fitar da gwani ba. Kotun kolin nigeria ce tayi hukunci cewa duk wanda yazo na biyu a babban zaben da aka gudanar to shine ya cencenta yazama gwamna saboda jam'iyar APC batayi sahihin zaben fitar da gwani ba. Yanada Mata 4 yaya kuma 29.

Suleiman Muhammad Maradun.

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye