Posts

Showing posts with the label rikicin boko haram

Ankashe Mutum 27,000 sanadiyyar rikicin Boko Haram

Image
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 27,000 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekara 10 na rikicin Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe. A farkon makon nan ne aka cika shekara 10 da kashe Shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf. Jami'in tsara ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon ne ya bayyana haka lokacin wani taro kan cika shekara 10 da fara rikicin, wanda aka yi a Abuja ranar Laraba. "Rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar tsakanin shekarar 2009 zuwa 2019 ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 27,000," in ji Mista Kallon kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa. . Kazalika, ya ce kimanin mutum miliyan biyu ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin. Ya kuma ce Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta ji dadin yadda aka kashe da kuma sace ma'aikatan agaji ba. Ya ce ma'aikatan sun mutu ne a bakin aiki, kuma "ba za mu taba mantawa da su ba." A ranar 3...