Posts

Showing posts from May, 2020

Abubuwa 10 masu mahimmanci a kwanaki 10 na karshen Watan Ramadan

Image
A daren Lailatul Qadri da ke goman karshe na watan azumin Ramadan ne Allah ubangiji ya saukar da Alkur'ani mai girma, abin da ya sa Musulmi suke neman dacewa da wannan daren. Duk da cewa babu tabbacin wane dare ne aka ware cewa shi ne daren na Lailatul Kadri, amma hadisai da malamai sun nuna cewa daren yana wakana ne a mara ta karshen kwana goma na watan Ramadan. Dararen mara dai kan fara tun daga daren 21 da daren 23 da 25 da 27 da kuma 29. Hakan ne ma ya sa wasu Musulmin yin tsumbure dangane da ibadun da ake son yi wato idan sun yi wannan dare sai su huta a wani daren inda za su sake kaimi a daren mara na gaba. To sai dai malamai sun ce ba a yi wa ubangiji wayo, inda suke shawartar masu neman dacewa da su raya dukkanin daren goman karshen azumin Ramadan: Dr Bashir Aliyu Umar wanda shi ne limamin masallacin Alfurqan da ke birnin Kano ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Kadri, kamar haka: 1. Niyyar neman yardar Ubangiji 2. Neman...