Posts

Showing posts with the label pdp

Zamukai Gwamnatin Zamfara Kara Kotu: Oshiomhole

Image
Shugaban jam'iyar Apc na Nigeria Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole ya ce jam’iyyar za ta nemi taimakon bangaren shari’a don kawo karshen ayyukan ta’addanci da musgunawa ‘ya’yan jam’iyyar a jihar ta Zamfara. Shugaban j am’iyyar ta APC ya ce dole ne a ba ‘yan jam’iyyar damar gudanar da ayyukansu cikin‘ yanci ba tare da wani nau’i na tursasawa da tsoratarwa daga gwamnatin PDP a jihar Zamfara ko wata jihar da ba su da gwamnoni ba. Oshiomhole ya yi magana ne lokacin da jam’iyyar reshen jihar Zamfara ta gabatar da takarda a gabanta tana zargin gwamnatin jihar da tilasta mambobinta, musamman zababbun shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisa su koma PDP. Oshiomhole ya kara da cewa a cikin dimokiradiyya mai dimbin yawa, dole ne a kyale kowa ya yi amfani da 'yancin walwalarsa. Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta zargi jam’iyyar PDP da jagorantar gwamnati da tirsasawa yayanta komawa PDP dakuma yin barazana ga wadand...

Laifin gwamnati ne matsalar tsaro a Najeriya- PDP

Image
Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce matsalolin da al'ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya sa rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki. Sanata Umaru Tsauri, sakataran kasa na jam'iyyar PDP ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC. Ya ce rashin fadar gaskiyar lamurra game da halin da kasa ke ciki daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka jefa kasar cikin halin rashin tsaron da take ciki. An yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan sa-kai da masu satar mutane Birtaniya za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta'addanci Ba mu gaza ba wajen yaki da masu satar mutane - Dambazau Ya ce "babu abin da ya jawo wannan matsala illa gwamnati ta ki yarda ta fadi wa mutane gaskiya cewa wannan abu na faruwa, kuma a dauki mataki." Ya kuma ce aikin gwamnati ne ta gano wadanda ke da hannu cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar tsaro a Najeriya, ba jama'ar kasar ba. Sanata Umaru Tsauri ya ce halin da Najeriya ...

KIRA NA MUSAMMAN GA YAN TAKARAR JAM'IYUN ADAWA NA JAHAR ZAMFARA

Assalamu alaikum, Al'amarin siyasar Zamfara yana matukar bani tsoro lura da irin yanayin tabarbarewar harkar tsaro a jahar nan. A fili take cewa gwamnatin APC mai mulki bata damu da halin da al'ummar Zamfara suke ciki ba, tafi damuwa da sha'anin siyasar ta bisa kula da kare rayukan mutane da dukiyoyinsu saboda haka a tunani na Insha-Allahu canza gwamnati shikadai ne mafita ga al'ummar jahar Zamfara amma dole sai su mutanen Zamfara sun tashi sunyi dagaske koda Allah zai taimakesu lura da irin taurin kai da nuna halin a mutu ko ayi rai akan rasa wannan mulki da gwamna mai barin gado yake dashi. Saboda haka naga ya dace inyi wannan kira ga manyan yan takararmu na jam'iyun adawa, kamar Hon. Bello Matawalle, Hon. Sani Abdullahi Wamban Shinkafi da Sanata Sa'idu Muh'd Dansadau da cewa su dibi halin da jahar Zamfara take ciki su ajiye adawar siyasa su hadu su marawa daya daga cikinsu baya domin ceto jahar Zamfara daga bala'in da take ciki. Dalilin d...