Posts

Showing posts with the label buhari

Kotun Koli ta bayyana dalilan korar karar Atiku da PDP

Image
Shugaba Buhari da Ministern Shari'a Kotun Kolin Najeriya ta ce Muhammadu Buhari "ya cancanci" ya yi takara a zaben shugaban kasa na watan Fabarairun 2019 sabanin ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa Buhari bai yi karatun sakandare ba. Kotun ta yi watsi da karar ne 'yan sa'o'i da fara sauraronta ranar 30 ga Oktoba ba tare da wani cikakken bayani ba, wadda Atiku ya shigar bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta sallami karar farko da ya shigar tun a ranar 11 ga Satumban 2019. Sai a yau Juma'a ne kotun ta ce za ta bayyana dalilanta na korar karar. Bisa wannan dalili ne kuma ta yanke hukuncin cewa korafin nasu bai karbu ba kuma ta kori karar tun a ranar 30 ga watan Oktoba. Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito Mai Shari'a John Okoro yana karanto hukuncin a madadin Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim Muhammad. Mai shari'a John Okoro ya ce gazawar masu korafin na gabatar da kwararan shaidu shi ne dalilin korar karar, inda suka ga...

Jerin tafiye tafiyen da shugaba Buhari yayi cikin shekara Hudu da Rabi

Image
Shugaba Muhammad Buhari Idan akwai wani batu da aka tayar da kura a makon nan, shi ne na tashin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Saudiyya domin halartar wani taron kasuwanci, inda daga nan zai wuce zuwa birnin Landan, kafin daga bisani ya koma Najeriya a ranar 17 ga Nuwamba. A ranar Asabar din nan ne ake sa ran Shugaba Buharin zai bar kasar Saudiyya zuwa Birtaniya domin kai wata ziyarar radin-kai inda zai kwashe kwana 17. Idan har Buhari ya koma Najeriya a ranar 17 ga watan Nuwamba, to lissafi zai kama kwanaki 425 ke nan shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekara hudu da rabi na mulkinsa. Gajerin tafiyeta da Sugaba Huharin uayi 2015 3 Yuni - Niamey - Niger - Taron koli kan Boko Haram (tafiyar Buhari kasar waje ma7ko guda bayan shan rantsuwa) 4 Yuni - N'Djamena - Chad - Ziyarar aiki 7 - 8 Yuni - Munich - Germany - Taron koli na kasashen G7 na 42 12 - 13 Yuni - Johannesburg - Afirka ta Kudu - Taron Tarayyar Afirka na 25 19 - 23 Yuli - Washington, D.C. ...

Bazamu Bari akifar da Gwamnatin Buhari ba - 'Yan sanda

Image
Sufeton Yan sandan Nigeria Sifeton 'yan sandan, Muhammad Adamu a wani gargadi da rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na twitter, ya ce rundunar 'yan sanda ba za ta zura ido ga masu son kifar da zababbiyar gwamnati ba. Gargadin ya ce "rundunar 'yan sanda ta ga wani bidiyon da ke karakaina a soshiyal midiya wanda ya fito daga wata kungiya mai suna Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria and others', da ke tunzura 'yan Najeirya na gida da waje wajen shiga a dama da su a zanga-zangar yi wa gwamnatin Najeriya matsin lamba a ranar Litinin 5 ga watan Agusta da manufar kifar da gwamnatin." Rundunar da ta kara da cewa " Rundunar 'yan sanda na sanar da jama'a ba tare da shakku ba cewa wannan zanga-zangar daidai take da cin amanar kasa da aikin ta'addanci saboda haka rundunar ba za ta zura wa masu yunkurin yin hakan ido ba su tayar da zaune tsaye a kasa ba." Sifeto Janar ya kara da cewa "a...

Ya kamata ministocina su yi alfahari da kansu – Buhari

Image
Shugaba Buhari da Ministocinsa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa ministocinsa cewa ya kamata su yi alfahari da kasancewarsu wani bangare na "gwamnati mafi sanin makama". Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron majalisar ministoci ranar da ake yi duk ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja. Wannan dai shi ne zaman da shugaban ya yi a majalisar zartarwarsa na karshe da ministocinsa. Sai dai shugaban ya ba su damar ci gaba da aiki har zuwa 28 ga watan Mayu, inda za su mika takardar ajiye aiki ga sakataren gwamnati Boss Mustapha, kwana daya kafin a rantsar da sabuwar gwamnatinsa a mako mai zuwa. Da yake jawabi a cikin dakin taron, Shugaba Buhari ya ce sunayen ministocin ya shiga cikin tarihin Najeriya, wanda hakan abin alfahari ne. "Kowannenku yana da wata baiwa ta musamman kuma mu ne hoton Najeriya da muke fatan ginawa. Kasa mai kabilu da dama wadda kowanne dan kasa yake da 'yancin fadar albarkacin bakinsa. "Ya kamata ku yi alfahari da k...

Kalaman Buhari kan tsaro sun jawo ce-ce-ku-ce

Image
Sufeton 'Yan sanda, Shugaba Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban sufeton 'yan sanda kasar na kokari matuka wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar. Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo kasar bayan kwashe kwanaki 10 a birnin Landan. Shugaban ya ce "ga duk wanda ya san sufeton 'yan sanda to zai fuskanci ya rame sosai saboda tsabar aikin da yake yi." Hakazalika a lokacin da dan jaridar tashar talabijin din kasar NTA ya yi masa tambaya kan kafa sabuwar gwamnati, Buhari ya amsa da cewa "ba zan ce komai a kai ba." Sai dai wadannan kalaman nan shugaban sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kasar. Wasu suna ganin bai kamata shugaban ya yi su ba, ganin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a kasar da kuma yadda ake satar mutane don neman kudin fansa ba dare, ba rana a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna. Cikin kwanaki da shugaban ya shafe baya kasar an samu matsaloli tsaro da dama da garkuwa ...

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Image
Shugaba Muhammadu Buhari A shekarar 2003 da shugaba Buhari yafara tsayawa takara, jahar Zamfara sunyimai ruwan kuri'u a jam'iyarsa ta APP kuma itace jamiyar dake mulki a jahar Zamfara a wancen lokacin haka a 2007 bayan sauya sunan jam'iyar daga APP zuwa ANPP al'ummar Zamfara sunsake marama Buhari baya hakama a 2011 bayan barin jam'iyar ANPP yakoma CPC al'ummar Zamfara sun mara masa baya har yalashe zabe ajahar duk da ba itace jam'iyar dake mulkiba a jahar ba a wancen lokacin, haka kuma a 2015 bayan dunkulewar manyan jam'iyun adawa waje daya suka samarda jam'yar APC kuma suka aminta Shugaba Buhari Yatsaya masu takara, al'umma Zamfara basugajiba suka sake marawa shugaba Buhari baya har Allah yakaishi ga samun nasarar zama shugaban kasar Nigeria, bakomai yasa al'ummar zamfar ke goyon bayan Buhari ba sai saboda Gaskiya da rikon amanar da akasanshi dasu. Amma duk da wannan namijin kokarin da Al'ummar Zamfara sukayiwa Shugaba Buhari b...