Kotun Koli ta bayyana dalilan korar karar Atiku da PDP
![]() |
| Shugaba Buhari da Ministern Shari'a |
Kotun Kolin Najeriya ta ce Muhammadu Buhari "ya cancanci" ya yi takara a zaben shugaban kasa na watan Fabarairun 2019 sabanin ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa Buhari bai yi karatun sakandare ba.
Kotun ta yi watsi da karar ne 'yan sa'o'i da fara sauraronta ranar 30 ga Oktoba ba tare da wani cikakken bayani ba, wadda Atiku ya shigar bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta sallami karar farko da ya shigar tun a ranar 11 ga Satumban 2019.
Sai a yau Juma'a ne kotun ta ce za ta bayyana dalilanta na korar karar. Bisa wannan dalili ne kuma ta yanke hukuncin cewa korafin nasu bai karbu ba kuma ta kori karar tun a ranar 30 ga watan Oktoba. Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito Mai Shari'a John Okoro yana karanto hukuncin a madadin Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim Muhammad.
Mai shari'a John Okoro ya ce gazawar masu korafin na gabatar da kwararan shaidu shi ne dalilin korar karar, inda suka gabatar da shaidu biyar kacal cikinsu har da babban mai bayar da shaidar, wanda shi kuma ya bayyana jita-jita a matsayin shaida.
Ya kara da cewa kazalika sun gaza gabatar da hujjar zargin da suka yi na yin aringizon kuri'u - sun gaza gabatar da takardar sunayen masu zabe domin tabbatar da hakan.
Saboda haka Mai Shari'a Okoro ya ce hukuncin na yau (Juma'a) ya jaddada wanda kotun sauraron kararrakin zabe ta yi ranar 11 ga Satumban 2019, wadda ta tabbatar da zaben Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

Comments
Post a Comment