Posts

Showing posts with the label abdulmuminu jibrin

APC ta dakatar tare da neman a kori Abdulmumin Jibrin Kofa

Image
Abdulmuminu jibrin Jam'iyyar APC a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano ta kori dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, tare da neman uwar jam'iyyar ta kore shi gaba daya. A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bebeji, Suleiman Gwarmai, ya sanya wa hannu, ya ce an dakatar da dan majalisar mai wakiltar ne a mazabarsa, saboda yana yi wa jam'iyyar zagon-kasa. Alhaji Suleiman ya ce an dauki matakin ne bayan da wani kwamiti mai mutane bakwai da jam'iyyar ta kafa bayan da ta samu korafi a kan dan majalisar, ya yi bincike ya kuma mika rahotonsa. Kawo Abdulmumini Jibrin bai mayar da martani ba kan wannan sanarwa. BBC ta tuntube shi a waya amma bai amsa kiran ba. A baya-bayan nan dan majalisar ya samu kansa cikin rikicin siyasa tsakaninsa da wasu gaggan jam'iyyar a Kano. Kuma rahotanni sun ambato shi yana cewa yana shirin barin majalisa domin komawa jami'a saboda yana so ya zama farfesa. Y...