''Yan fashi sun kashe sama da mutum 30 a Zamfara'
Hanyar Dan Sadau a Zamfara Sarkin Kudun Dan Sadau a jihar Zamfara ya shaida wa BBC cewa 'yan fashin daji sun kashe sama da mutum 30 lokacin da suka auka wa kauyen Dan-Gurgu na masarautarsa tare da jikkata karin wasu 12. Alhaji Hussaini Umar ya ce dukkan mutanen da abin shafa maza ne, wadanda aka far wa a lokacin da suke haramar tafiya gonakinsu wayewar garin ranar Asabar. Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammed Shehu ya ce mutum goma aka kashe yayin wannan hari, tare da jikkata karin wasu hudu. Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan fashin daji, wadanda kan far wa kauyuka, su kashe mutane, tare da kona gidajensu har ma da dukiyar da suka mallaka. Ko da yake da farko sun fara ne da satar mutane, inda sukan rike su har sai dangi ko makusantansu sun biya kudin fansa. Masarautar Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru ta yi makwabtaka da yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, wanda ya yi kaurin suna ...