Anbaiwa Gwamna Bello Matawalle kyautar jinjinawa
Gwamna Bello Matawalle A Shafinsa na sada Zumunta na facebook Babban Mai taimakawa Mai girma gwamna Bello Matawalle akan yada labarai ya wallafa cewa: Wata kungiya mai zaman kanta wacce aka fi sani da suna Noble Women Initiative for Sustaining Democracy (NWISD) a Ranar Talata 10/09/2019 ta gabatar da kyautar yabo bisa shugabanci ga mai girma gwamna Bello Matawalle. Da take gabatar da kyautar, shugabar kungiyar, Misis Maryam Sama'ila ta ce kungiyar ta amince da kyakkyawan jagoranci na gwamna Matawalle musamman jajircewarsa ga tsaro da nasarorin da ya samu a cikin dan kankanen lokaci. Gwamna Matawalle ya godewa kungiyar bisa wannan kyautar sannan ya sake jaddada kudirin sa na kara yin aiki domin kawo cigaba a Zamfara da Najeriya baki daya. Suleiman Muhammad Maradun📝