Muhimman abubuwan a kwanaki 10 na farkon Dhul Hajji.
Alqur'ani maigirma Hadisin manzon tsira (SAW) ya tabbatar da cewa babu wani aikin ibada da yafi girman daraja fiye da a cikin wadannan kwanakin. Imamu dabarani yaruwaito cewa Manzon Allah (s a w) yace; acikin kwanakin shekara akwai wasu kyaututuka na ubangiji, kuyi kokari kusamesu, Yana yuyuwa idan wani budi yasami dayanku acikinsu to har abada bazai sake tabewa ba. Gakadan daga cikin Abu buwan da Ranakun suka kunsa. 1) Allah ya yi rantsuwa da kwanaki goman Dhul-Hijja a cikin suratul fajari sura ta 89 aya ta 1-2. 2) Sune kwanakin da ake kira “AYYAMIN MA’ALUMAT” (kwanaki sanannu) : Allah yayi umurni ga muminai da su ambace sa a cikin kwanaki sanannu (Al-Haj:28) ayi zikiri saboda ni'imar Allah na dabbobin da ake yankawa na Hadaya da Layya. 3) Wadan nan kwanakin suna cikin arba'una na Musa Wanda Allah kecewa katuna lokacin damukayi na haduwa, bayan cikar kwana 30 nafarko ubangiji yacemsa Yakoma yacika 10, wadannan sune kwana 10. 4) Ana ninka ladan aiki na kwarai nink...