Kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye

Sanata dino melaye
Kotun sauraron kararrakin zabe a garin Lokaja na jihar Kogi ta soke zaben Sanata Dino Melaye, wanda yake wakiltar shiyyar Kogi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.
Yayin zaman kotun na ranar Juma'a ne aka soke zaben kuma aka umarci sake sabon zabe a shiyyar.
Daya daga cikin mutanen da suka kalubalanci Mista Melaye ne wato Sanata Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ya shigar da kara a gaban kotun.
Bayan yanke wannan hukuncin Sanata Melaye ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Sanata Melaye ya fara zama dan majalisar wakilan kasar ne a shekarar 2007, inda yake wakiltar mazabar Kabba da Ijumu da ke jihar Kogi.
Sai da ya yi wa'adi biyu a majalisar wakilai kafin ya lashe zaben dan majalisar dattawa a shekarar 2015.
Kazalika a watan Yuni ne ya bayyana muradinsa na shiga takarar neman gwamnan jihar Kogi, wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye