Yakamata a yi wa Zakzaky adalci – Sheikh Bala Lau

Bala Lau
Shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi wa jagoran 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky adalci.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne lokacin da yake hudubarsa ta Juma'a a masallacin hedikwatar kungiyar ta JIBWIS da ke Utaku a Abuja ranar Juma'a.
Ba wannan ne karon farko ba da wani babban malamin sunnah a kasar yake magana kan batun jagoran 'yan Shi'a a kasar.

Sheikh Ahmad Gumi ya taba kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sake shi a baya.
Malamin ya ce: "Babu wanda ba ya son a yi wa shugabansu (Zakzaky) adalci. Ko kafiri ne a yi wa adalci. Idan abin da ya yi ba daidai ba ne a hukunta shi saboda gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah."

Ya ci gaba da cewa: "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi abin da suka ga dama domin a saki shugabansu.
"Daga nan babu sauran zaman lafiya kenan," in ji shi.

Kazalika, ya ce "idan jagoran 'yan Shi'an bai yi laifi ba, to a sake shi. Idan ko ya yi laifi a yi masa hukunci kamar yadda ake yi wa kowane dan kasa mai laifi. "Idan aka yi haka an zauna lafiya."
Ya kuma kara da cewa ba ya jin dadin yadda wasu suke kokarin siyasantar da batun.

Ya ce: "Akwai wasu da suke kokarin yin amfani da matsalar wajen hada 'yan Izala fada da 'yan Darika a Najeriya. Suna cewa idan aka gama da 'yan Shi'a su za a koma wa."

A gefe guda kuma, shugaban kungiyar ya soki yadda BBC ta yi kuskuren danganta Muhammad Yusuf tsohon shugaban Boko Haram da jami'ar Musulunci ta Madina a wani rahoto da ta wallafa ranar Talata.

Labarin an wallafa shi ne saboda cika shekara 10 da aka yi da fara rikicin Boko Haram a Najeriya.
Sheikh Bala Lau ya yi kira ga BBC din da ta gaggauta gyara kuskuren da ta yi.

Sai dai tuni BBC ta gyara wannan kuskure 'yan sa'o'i bayan wallafa labarin kuma ta nemi gafarar jama'a.

Rohoton Sashen Hausa na Bbc.

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye