Nasha alwashin karbo Naira biliyan 90 hannun Yari: Matawalle
![]() |
| Gwamnan jihar Zamfara |
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi alwashin dawo da sama da N90bn daga tsohon gwamna Abdulaziz Yari wanda ake zargin ya karkatar da shi ta hanyar hauhawar farashin kwangila.
Matawalle, wanda ya yi jawabi a lokacin gabatar da rahoton wucin gadi daga kwamitin tabbatar da ayyukan na jihar, ya jaddada cewa zai tabbatar da cewa an maido da kudaden da aka karkatar a tsohuwar Gwamnatin Yari.
Gwamnan ya ce, "Zan aiwatar da rahoton kwamitin don tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a badakalar.
Tun da farko, shugaban kwamitin, Alhaji Ahmed Zabarma, ya fada wa gwamnan cewa kwamitinsa ya gano wasu makudan kudade da aka karkatar yayin gudanar da ayyukan Yari, yana mai kira ga gwamnan da ya kafa kwamitin bincike don karbar kudin.
Zabarma ya ce tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, gwamnatin Yari ta ba da kwangiloli 6,180 a wurare daban-daban a cikin jihar "inda da yawa daga cikin kwangilolin ba ayisu yanda yakamata ba ko kuma ba a yi su kwata-kwata ba, yayin da aka riga akabiya kudaden."
Suleiman Muhammad Maradun
08139275969

Comments
Post a Comment