TARIHIN MALAM ISAH ALI PANTAMI
![]() |
| Dr. Isah Ali Pantami |
An haifi Malam Isah Ali Pantami ranar 20 ga watan goma (October) shekarar 1972 a garin Gwambe dake Nigeria, shekarunsa 46, sunan mahaifiyarsa Hajiya Amina Umar Aliyu, mahaifinsa Alhaji Ali Ibrahim Pantami. Yafara karatu a makarantar allo tareda hardar al qur'ani Mai girma, yashafe fiye da shekara hudu a makarantar allon kafin daga bisani asakashi primary a garin Pantami, yayi karatunsa na sakandiri a Goverment science Secondary schools dake Gwambe. Bayan kammala sakandiri yashafe shekara biyu Yana karatun addini kafin daga bisani ya halarci Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi, inda yasamu digirinsa ta daya data biyu (Bsc,Msc) a fannin Fasahar kwamfuta a shekarun 2003 da 2008, daga bisani kuma yaje Jami'ar Robert Gardon a Aberdeen dake kasar Scotland inda yasamu digirinsa ta ukku (PhD). Yashafe gabada daya rayuwarsa akan karatun addini Dana Zamani.
Malaman dayayi koyon karatu wajensu sun hada da; Muhammad Umar fallata, Muhammad ibn al uthaymeen, da Abdulmuhsin ibne Abbad.
Malam Isah Ali Pantami, malami (Lecturer) ne a Jami'ar Abubakar Tabawa Balewa dake Bauchi a fannin Information Technology, kafin daga bisani malami (Lecturer) a Jami'ar musulunci dake Madina a matsayin Shugaban masu rubutun fasaha (Head of Technical writing) a 2014. A shekarar 2016 shugaba Muhammadu buhari yanadashi shugaban National information Technology development agency (NITDA). Yasamu kyaututuka daban daban dazasu Kai 50 acikin shekara biyu.

Malam Isah Ali Pantami yashafe fiye da shekara ashirin (20) Yana limancin sallar jumu'a anan Nigeria dakuma kasar England. Yayi aiki a matsayin member a hukumar Shari'a ta Ja'iz bank. Yakuma Zama mataimakin sakatare na majalisar koli kan Shari'a na kasa (supreme council for Shari'a). Yazama Shugaban hukumar amintattu na al'huda islamiyya & mosque foundation. Yakuma Zama members a Kwamitin dattawa masu bada shawara na Jihar Bauchi.
Yatabayin muhawara da tsohon Shugaban kungiyar Boko Haram na wancen lokaci Muhammad Yusuf a 2008. Malam yarufuta littafai dazasu Kai Akallah 12 akan Fasaha, addini, dakuma siyasa. Yakuma wallafa jonal fiye da 20 a fannoni daban daban. A ranar 23 ga watan juli Sunan Malam Isah Ali Pantami yafito cikin jerin sunayen da shugaba Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawan Nigeria domin tantancesu a matsayin wadan da zai nada a matsayin Ministocinsa.

Suleiman Muhammad Maradun

Allahu Akbar,Allah karawa malan lafiya da basira, mukuma Allah karo muna ilimin duniya Dana lahira damu da malan gabakidai
ReplyDelete