Banbancin Gwamnatin Matawalle data Audu Yari

Gwamna Bello Matawalle
Tun bayan rantsar dashi amatsayin Gwamnan jihar Zamfara Acikin sati daya da bashi mulki Gwamna Matawalle yaziyarci yankin Mada Wanda yakunshi Gurbin bore da Wonaka dake karamar hukumar mulkin Gusau, wannan yanki, yankine da yayi fama da hare, haren Yan bindiga da barayin shanu, Amma a tsohuwar Gwamnatin data gabata Babu wani jami'in tsohuwar Gwamnatin daya taba koda kaimusu ziyara koda da niyar yimusu jaje, Amma Bello Matawalle yataka da kafarshi yaje wannan yanki yakuma Basu alwashin za'a magance wannan matsala cikin kankanin lokaci. Haka kuma yakai irin wannan ziyara a yankin kanoma dake karamar hukumar Maru  yaji korafe, korafen da al'ummar wanan yanki suke dasu wanda hakan yasa aka dakatar da sarkin na Maru dakuma hakimin Kanoma bisa zarginsu da alaka da Yan bindiga, Wanda yake tsohuwar Gwamnati Bata taba irin wannan kokariba.

A tsohuwar Gwamnatin data gabata ankashe mutum fiye da dubu biyar (5,000) anraunata fiye da mutum dubu goma anbiya kudin fansa dazasu haurama naira biliyan bakwai 7,000,000,000 an lalata filayen noma masu yawa anmaida kananan yara marayu da zasukai dubu goma 10,000  anmaida matan aure zawarawa da yawansu zaikai dubu hudu 4,000 kuma duk da haka Babu wani taimako da tsohuwar Gwamnati tayiwa wayan Nan al'umma. Kai ko magana Mai dadi tsohon Gwamna bazai makuba bare kuji dadi, bazan manta lokacin da annobar amai da gudawa ta barke  a Zamfara ba Gwamna Yari yace Zunuban Yan Zamfara ne yajamuna wannan annobar. 

Amma acikin wata biyu na mulkinsa Gwamna Matawalle sanadiyar sulhun dayayi da barayin shanu ankubutar da rayukan mutum fiye da dari ukku 300 ayankuna daban, daban na jihar Zamfara Kai harda makwabtan jihar, Babu ko sisin kwabo, Wanda yake ankare hasarar kudi da yawansu zai'iya kaiwa naira miliyan dari Tara (900,000,000) da za'a biya a matsayin kudin fansa, rayukan Mata, kananan yara, da yan'uwa sunyi farinciki sanadiyar dawowar Yan uwansu a cikin iyalansu.

Matasa sune kashin bayan al'umma Amma sunacikin nagaba gaba dasukasha bakar wahala alokacin mulkin Gwamna Yari ta fannona daban daban, acikin shekarun takwas 8 na mulkin Yari sau dayane yataba bada taimakon kudin karatu ga makarantun gaba da secondary (scholarship) a 2012 sannan aduk shekara fiyeda mutum dubu biyu 2,000 ne ke kammala karatunsu tsakanin Diploma, NCE, da Degree, Amma Gwamna Yari harya Sauka baidauki kowa aiki ba.
Amma cikin kwanaki kadan dabashi mulki Gwamna Matawalle yayi alkawarin zaisamarda ilmi kyauta a fadin jihar Zamfara. Kuma za'a fitar da  wasu matasa tsallake Domin susamo ilmi kyauta, sannan tun ajawabinsa na rantsarwa Gwamna Matawalle yace ma'aikata 1,400 da tsohuwar Gwamnati ta dauka takasa biyansu albashi fiye da shekara biyar to yadawo dasu aiki, yanzu haka anashirye shirye don fara biyansu albashi, sannan Gwamna Matawalle akarkashin ma aikatar Nan dayasamar ta Zamfara Social intervention program (ZASIP) zai Samar da ayukanyi ga matasa guda dubu ukku da dari takwas 3,800 akananan hukumomi goma Sha hudu 14 dake jihar Zamfara.

Bagaren ma'aikatan gwamnati kuma tsohuwar Gwamnatin data gabata ta Abdul'aziz Yari bayan kin daukar ma'aikata datayi takasa biyan mafi karancin albashi na dubu goma Sha takwas, duk a fadin Nigeria Jahar Zamfara ce kadai ma'aikatan ta ke karbar mafi karancin albashi dubu bakwai da dari biyar 7,500. Amma tun alokacin yakin neman zaben Gwamna Matawalle yayi alkawarin biyan mafi karancin albashi na dubu talatin 30,000 daza'a aiwatar Nan bada dadewa ba. Tsohuwar Gwamnatin A.A Yari takasa biyan ma aikatan dasuka ajiye aiki yakasa biyansu hakkokansu, sunfitar da kudin Amma suka sace kafin sutafi, Amma muna kyautata zaton wannan Gwamnati zata biyasu hakkokansu bada dadewa ba saboda yanda mukaga kamun ludayin Gwamnatin. 
Akwai abubuwa da yawa da wannan Gwamnati ta aiwatar nacigaba Amma zamu hadu a ruhutu na gaba.

Suleiman Muhammad Maradun.

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye