Miyasa 'Yan Zamfara Sukayi Murna da Hukuncin Kotun Sokoto
Ranar 25/03/2019 kotun daukaka kara dake Sokoto ta jingine hukuncin kotun tarayya dake Gusau wacce tayi hukunci cewa jam'iyar APCn jahar Zamfara tayi zaben fitar da gwani saboda haka hukumar INEC takarfi sunayen yantakararta, sunayen da hukumar INEC tace bazata karba ba tundaga farko saboda shedar da tasamu cewa jam'iyar batayi zaben fitar da gwani ba. Kotun dake sokoto tace kotun ta Gusau batayi nazari akan hujjojin da aka gabatar mata ba kafin tayi hukunci ". Bayan yin wannan hukunci na kotun ta Sokoto sai nalura da cewa mafiyawan al'ummar Zamfara sai murna sukeyi da wannan hukunci kama daga Talakawa, Dalibai harma da ma aikatan gwamnati. naga farinciki afuskokin jama'a da yawa kuma duk inda kazagaya afadin jahar, firarce zakaga anayi. Dalilin wannan farinciki na al'umma Zamfara da wannan hukunci shine Gwamnatin dake mulki wacce wannan hukunci zaisa takai garasa mulkinta, ta yaudari al'ummar jahar Zamfara kama daga Talakawa, yan boko, yankasuwa,...