YAUSHE GWAMNATIN ZAMFARA ZATA BIYA KUDIN NECO 2018

Daga hagun Daliban secondary, Gwamna yari
Jahar Zamfara tana daya daga cikin jihohi mafi ci baya a bangaren ilmin zamani saboda sakacin da Gwamnatin A.A Yari keyi da harkar ilmin. Gwamantocin da suka gabata a jahar Zamfara sun taka rawar gani sosai bangaren ilmi ajahar saboda babu jarabawar daza ayi face anbiya kudin jarabawar kafin fitowarta.

Amma a wannan gwamnati abun babu wani cigaba kullun al'amarin jihar Zamfara sai kara tabarbarewa yakeyi. Daga shekarar 2014 ne dalibai a Zamfara suka san a saki sakamakon jarabawa amma ba'a biya kudi ba a 2014 saida jarabawar NECO tayi fiye da shekara biyu gwamnati bata biya kudi ba, haka ya faru a 2015, 2016 da 2017; haka kuma haryanzu da nake wannan rubutu babu wani bayani mai gamsarwa gameda jarabawar NECO ta 2018.

Shin nawa ne kudin jarabawar? da har zasu gagari gwamnati biya idan muka lura da makudan kudaden da gwamnati take kashewa a wajen campaign dawasu ababenda basuda wani amfani ga cigaban jaha, kawai dai a fili take gwamnatin A.A Yari bata damu da harkar ilmi ba.

Duk lokacin da akace jarabawar WAEC ko NECO ta fito zakaga yayan masu hannu da shuni sunata rigwangwoniya wajen duba sakamakonsu, amma yayan talakawa a Zamfara saidai kaji suna fadar cewa mu ko sai yaushe Gwamnati zata biya kudinmu?
Saboda haka Gwamnati taji tsoron Allah ta tausayawa yayan talakawa dake karatu a makarantun Gwamnati ta rika biyan kudin jarabawarsu akan lokaci domin suma su shiga tsara wajen zuwa makarantun gaba ga secondary; yin hakan zai taimaka sosai wajen magance matsalar tsaron da Jahar Zamfara take fama dashi da kuma shan miyagun kwayoyi da matasa suke fama dashi.
Allah Yasa wannan kira nawa ya samu karbuwa Ameen.

Suleiman Muhammad Maradun.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye