Gwamna Matawalle ya kafa kwamitin tsara dabaru da ci gaban jihar Zamfarawa

Gwamna tareda yan Kwamiti

A Ranar laraba 11 ga watan satumba 2019 babban Mai taimakawa gwamna kan kafofin sadarwa ibrahim bello zauma ya wallafa a Shafinsa na facebook cewa:

A kokarinsa na bayyana manufofin Gwamnatinsa da samar da ingantacciyar hanya don biyan bukatun Yan jaharsa, Mai Girma gwamna (Dr.) Bello Matawalle ya kafa kwamiti mai karfi wanda zai jagoranci tsarin tsara dabarun ci gaba da kuma bunkasa cigaban jihar.

Kwamitin dai an kirkireshi ne a hankali wajen zaben ingantattun masu ba da ilimi da kuma mahimman horo game da dabarun, tsari da gudanarwa.  An ba kwamitin izinin aiwatar da wadannan ayyukan kamar haka:

1. Kirkiro da tsarin Ci Gaban shekara (2020-2030) ga jihar.
2.  Cigaba ta Bangaren tsare tsare da cigaban jiha.
3. Tattaunawa da MDAs na gwamnati, abokan tarayya na kasa da kasa don samar da tallafi ga jihar
4. Shawara ga gwamna kan al'amuran dabaru da ci gaban jiha.
5. Shawara mai Girma Gwamna bisa kyakkyawan tsari ga sabuwar Jami’ar Jihar Zamfara da kuma ci gaban dukkan makarantun da ke jihar.
6. Zakulo da wasu ayyukan da gwamna zai aiwatar.

Wadan da ke cikin membobin Kwamitin sunhada da:

 1. Farfesa Yusuf M. Adamu Tsafe - Shugaba
 2. Farfesa Yahaya A. Zakari - Mataimakin Shugaba
 3. Alhaji Musa Ahmed Bungudu - Memba
 4. Jalaludeen Ibrahim Maradun - Memba
 5. Barr.  Fatima Nahuche - Member
 6. Dr. Bashir M. Maru - Memba
 7. Gazali Shehu Ahmad - Sakatare

YUSUF M. ADAMU TSAFE malami ne a fannin Geography kuma tsohon Daraktan tsare tsare na Jami’ar Bayero Kano;

YAHAYA ABDULLAHI ZAKARI farfesa ne a fannin bunkasa tattalin arziki kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya da ke Gusau;

ALHAJI MUSA AHMED BUNGUDU ma’aikacin diflomasiya ne mai ritaya wanda ya yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya (a kasashe daban-daban) tsawon shekaru 32;

JALALUDEEN IBRAHIM MARADUN malami ne a jami'a kuma mataimakin Dean na sashen kula da dalibai, a Jami'ar Tarayya- dake jihar kebbi kuma a halin yanzu mai bincike ne a wata jami'a a Norway;

BARR.  FATIMA ABUBAKAR NAHUCHE lauya ce kuma Alkali a Kotun daukaka kara ta FCT;

DR.  BASHIR M. MARU likita ne na wata asibiti dake a Abuja kuma kwararre a fannin Lafiya Jari;  kuma.

GAZALI AHMAD SHEHU masani ne kuma kwararre a fannin Nazarin Ci gaba da Binciken Tsarin Mulki a halin yanzu yana aiki ga Tarayyar Inshorar Haraji ta Tarayya.

Kwamitin zai yi ganawa tare da Ma'aikatar zartarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha a kai a kai don tattaunawa kamar yadda ya cancanta, don daidaita alkiblar tsarin dabarun.

Ofishin mai ba da shawara na musamman ga gwamna mai aiwatarwa kan dabarun ci gaba tare da hadin gwiwar ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar za su taka muhimmiyar rawa a wannan aikin ta hanyar tarurruka da sauran hanyoyin shiga tsakani.

A yayin aiwatar da aikin, gwamna Matawalle ya roki membobin kwamitin tsara dabaru da ci gaban jihar Zamfara da suyi aiki da bukatun jihar ta Zamfara baki daya, tare da yin taka tsantsan game da matsalolin da gwamnati take samu, da zurfin masaniyar abubuwan da ke faruwa da kalubale a jihar.  domin hankali zamu sake gina jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya nuna godiyarsa ga mambobin kwamitin bisa yarda su shiga cikin wani tsari da zai tsara hanyar jihar nan da shekaru masu zuwa, kuma ya kara musu fatan Allah ya shiryi jagorar su wajen sauke nauyin da ke kansu.

Fassarar Suleiman Muhammad Maradun

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye