Gwamnan Jihar Zamfara zaigabatar da bukata a Majalisar dinkin Duniya
![]() |
| Gwamna Bello Matawalle |
Darakta Janar na Kamfanin labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara YUSUF IDRIS GUSAU ya bayyanacewa:
Mai Girma, Gwamnan jihar Zamfara Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) ya bar Nigeria, a 21 ga Satumbar, 2019 don halartar Babban Taron ƙasashen Afirka wanda zai gudana a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, United State of Amurka.
Matawalle ya bar ƙasar daidai da ƙarfe 8:21 na safe ta tashar Nnamdi Azikwe International Airport, Abuja a kan jirgin British Airways.
Taron Majalisar Dinkin Duniya na bana (UNGA) na wannan shekara zai gudanar da Babban Taron Zuba Jarin Nahiyar Afirka inda Gwamnan Jihar Zamfara zai gabatar da takarda mai taken "Tsarin Zuba Jari da Kasuwar Jihar Zamfara: don neman Hadin gwiwar Kasashen Duniya" ga masu saka jari na duniya a kan dinbin albarkatun ma'adinai da kuma buƙatar haɗin gwiwar Domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
A yayin Babban Taron saka hannun jari gwamna zai nuna babban ci gaban jihar ta Zamfara a yankin Saharar Afirka da kuma iyawar ta na tafiyar da karuwar karfin tattakin arziki da yake yawo a manyan sassan jihar.
Ana sa ran Gwamnan zai yi wata ganawa ta kwanaki biyu tare da Makarantun Kasuwanci a kasar Ingila tsakanin ranakun 22 zuwa 23 ga Satumba, 2019 don tsara yadda za a saka hannun jari a bangarorin samar da ababen more rayuwa, Ilimi, Aikin Noma, Kiwon lafiya, Masana'antu, karfafawa da kuma samar da ayyukan yi.
Tawagar jihar ta Zamfara zuwa Majalisar Dinkin Duniya a babban Taron Kasuwancin Afirka (UNGA) karo na 74 da za su kasance a cikin Babban Taron Kasuwancin Afirka sun hada da Shugaban Ma'aikata, Alhaji Kabiru Balarabe, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin, Col Bala Mande (Rtd), Mashawarci na Musamman ga Gwamna akan ci gaban Ma’adanai, Dakta Nura Isah Gusau da Sanata Lawali Hassan Daniya.
Ana sa ran Gwamna zai dawo gida a ranar 28 ga Satumbar, 2019.
Suleiman Muhammad maradun

Ma shaa Allah, muna fatan Allah ya qara Wa Gomnan mu (Hon. bello Matawalle) lafiya da kwarin guiwa, Allah ya Kare shi daga dikkan sharri, kuma Allah ya bashi nasara akan wannan tafiya, ya dawo mana da shi gida lafiya bijaahi ANNABI S A W.
ReplyDeleteAmeen ya Allah
ReplyDelete