CISLAC ta yaba wa Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Gwamna Bello Matawalle
Kungiyar Nan mai fafutukar yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya, CISLAC ta ce matakin da gwamnan jihar Zamfara ya dauka na soke dokar da ta amince a bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakansu fansho abun a yaba ne.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi koyi da jihar ta Zamfara wajen ganin an rage kashe kudaden gwamnati.
Kungiyar ta kuma nemi sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da gwamnan na Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce zai yi amfani da fanshon tsoffin gwamnoni da ya soke wajen raya karkara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin ya fitar, gwamna Matawalle ya yi takaicin yadda tsohon gwamna ya ke neman a biya shi makudan kudade a dai-dai lokacin da sauran 'yan fansho a jihar ke cikin kangin wahala saboda rashin biyan su kudadensu.
Ya kara da cewa 'yan fansho na bin gwamnatin da ta shude bashin kudade da suka kai naira bilyan 10.

Suleiman Muhammad Maradun
08139275969

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye