Matsayar Gwamnonin Nigeria akan Karin albashi na N30,000

Taron kungiyar gwamnonin Nigeria
Gwamnonin jihohi 36 a Najeriya sun ba da sanarwar cewa sun yanke shawarar biyan mafi karancin albashi na N30,000 na wata-wata.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi magana da manema labarai a Abuja ranar Alhamis a sakatariyar kungiyar.
Gwamnonin duk sun nuna ba tare da wani kace naceba wadanda muka yiwa dokar da suka zartar kan mafi karancin albashi. Babu wata muhawara, mun yarda da biyan Kudin ”, in ji Fayemi.


Tattaunawar damukayi tana magana ne  game da tasirin sakamako kuma kowace jiha ta fara aiwatar da hakan.
"Idan NLC ba ta da cikakkiyar masaniyar matsayin tattaunawar a cikin jihohi daban-daban za mu yi farin cikin bayyana bayanan da muke da su.
"Kodayake, yatsunsu ba daidai suke ba, jihohi dole ne su sasanta dangane da abin da zai biyo baya, za a iya samun jihohi wadanda zasu iya biyan N50,000,
Abinda zamu iya fada muku shine cewa ba wata jiha da zata biya kasa da, N30,000 idan muka kai ga matakin."
Suleiman Muhammad Maradun
08139275969

Comments

Popular posts from this blog

SHUGABA BUHARI NE YACI AMANAR YAN ZAMFARA

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye