Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye
![]() |
| Wasu Matasa dasuke Tattaki a Zamfar |
A ranar larabar ta gabatane wasu matasa suka gudanar da tattaki a babban birnin Jihar Zamfara dake Gusau, Akarkashin wata kungiya da wasu daga cikinsu suka kafa mai suna #Zamfara youths must survive ma'ana dole Matasan Zamfara susamu rayuwa mai kyau.
Sungudanar da tattakin ne daga Shataletalen tundun wada dayake a tsakiyar birnin Gusau zuwa majalisar dokokin Jihar inda suka gabatar da kukansu ga Majalisar domin ta kirkiro da wata doka wacce zata Hana sayarwa da duk danjihar Zamfara Magani idan batare da shedar likita ba.
Haka kuma suna bukatar Majalisar tahana sayar da Magani da daidaikun mutane keyawo dashi wadanda akafisani da Chemist a kafada sanna kuma Majalisar ta tanadi wata doka mai mai karfi ga duk Wanda aka kama Yana sayar da miyagun kwayoyi.
Amma saidai samun gabatar da wannan bukata tasu yaci tura bayan wata 'yar hayaniya data barke aharabar Majalisar wacce wasu yaran Yan siyasa suka tayar Amma kungiyar sungabatar da wannan bukata tasu arubuce.
Bayan barin harabar Majalisar dokokin ayarin 'ya 'yan kungiyar sunyi tattaki zuwa Fadar mai martaba sarkin Katsinan Gusau Alh Ibrahim Bello domin su shedamai irin kudurin dasuke dashi nason ganin Matasa sundena tu'amali da miyagun kwayoyi domin su inganta rayuwarsu.
Bayan isarsu afadar Mai martaba Sarki yayi maraba da wannan ayarin Matasa yakuma nuna matukar jindadinsa akan Wannan hangen nesa da Matasan sukayi sannan ya umarcesu dasudage domin wannan bakaramin aikine zasuyiba, sannan yayi alkawalin basu duk wata gudumuwa dasuke Bukata kuma yayi addu'ar fatar alkhairi garesu.
Shugaban kungiyar Abulhamid yaron Malam tare da sakataren kungiyar Ubaidullahi Yahaya Kaura Sunyin jawabin godiya ga dukanin 'y'yan kungiyar kuma sukayi fatar Allah yamaida kowa gidansa lafiya.
Sulaiman Muhammad Maradun
08139275969


Gaskiya Yayi Dai
ReplyDeleteMashaallh Allah yatabbatar dawannan qudurin
ReplyDeleteAmeen ya Allah
ReplyDeleteAllah ya kare matasa daga yin shaye-shaye amen.
ReplyDeleteAllah ya tsare Marassa yi, masu Yi Kuma Allah y sa sudae na amen.
ReplyDelete@Abdulrahman Bala BG (ABG TSAFE).