Posts

Matsayar Gwamnonin Nigeria akan Karin albashi na N30,000

Image
Taron kungiyar gwamnonin Nigeria Gwamnonin jihohi 36 a Najeriya sun ba da sanarwar cewa sun yanke shawarar biyan mafi karancin albashi na N30,000 na wata-wata. Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi magana da manema labarai a Abuja ranar Alhamis a sakatariyar kungiyar. Gwamnonin duk sun nuna ba tare da wani kace naceba wadanda muka yiwa dokar da suka zartar kan mafi karancin albashi.  Babu wata muhawara, mun yarda da biyan Kudin ”, in ji Fayemi. Tattaunawar damukayi tana magana ne    game da tasirin sakamako kuma kowace jiha ta fara aiwatar da hakan. "Idan NLC ba ta da cikakkiyar masaniyar matsayin tattaunawar a cikin jihohi daban-daban za mu yi farin cikin bayyana bayanan da muke da su. "Kodayake, yatsunsu ba daidai suke ba, jihohi dole ne su sasanta dangane da abin da zai biyo baya, za a iya samun jihohi wadanda zasu iya biyan N50,000, Abinda zamu iya fada muku shine cewa ba wata jiha da zata biya kasa da,...

Wasu Matasa a Zamfara sun Lalubo Hanyar da Matasa Zasu rage Shaye Shaye

Image
Wasu Matasa dasuke Tattaki a Zamfar A ranar larabar ta gabatane wasu matasa suka gudanar da tattaki a babban birnin Jihar Zamfara dake Gusau, Akarkashin wata kungiya da wasu daga cikinsu suka kafa mai suna #Zamfara youths must survive ma'ana dole Matasan Zamfara susamu rayuwa mai kyau. Sungudanar da tattakin ne daga Shataletalen tundun wada dayake a tsakiyar birnin Gusau zuwa majalisar dokokin Jihar inda suka gabatar da kukansu ga Majalisar domin ta kirkiro da wata doka wacce zata Hana sayarwa da duk danjihar Zamfara Magani idan batare da shedar likita ba. Haka kuma suna bukatar Majalisar tahana sayar da Magani da daidaikun mutane keyawo dashi wadanda akafisani da Chemist a kafada sanna kuma Majalisar ta tanadi wata doka mai mai karfi ga duk Wanda aka kama Yana sayar da miyagun kwayoyi. Amma saidai samun gabatar da wannan bukata tasu yaci tura bayan wata 'yar hayaniya data barke aharabar Majalisar wacce wasu yaran Yan siyasa suka tayar Amma kungiyar sung...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta Umarci Adamu Alieru daya dawomata da Naira biliyan 22

Image
Gwamna Bello Matawalle Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero da ya mayar da kudade sama da Naira biliyan 22  asusun jihar wandaaka yi zargin an samu daga kamfaninsa-Allied Trading Firm- a matsayin kudaden kwangilar don hade garuruwa 75 da kauyukan kasa a 2013. Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Engr.  Isah Mayana, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a karshen taron majalisar zartarwa ta jiha a gidan Gwamnati dake Gusau. Ya ce gwamnatin da ta gabata a karkashin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ce ta ba da kwangilar ta sama da Naira biliyan 25. Kwamishinan ya yi zargin cewa tun daga wannan lokacin, ci gaban ayyukan da kamfanin ya samu ya wuce kashi 60% kawai, don haka yazama dole gwamnatin yanzu ta gwamna Bello Mohammed Matawalle ta soke kwangilar. Majalisar zartarwa ta jihar ta hada baki daya ta amince da soke wasu kwangilolin guda biyu ta Naira biliyan 27 kowannensu. Su ne ayyukan samar da ruwan sha na karkara da aka bayar...

Majalisar Amurka ta tsige Shugaba Trump

Image
Shugaban Amurka Donald Trump 'Yan majalisar wakilai a Amurka sun jefa kuri'ar da ta tabbatar da tsige Shugaba Donald Trump, bisa wasu laifuka guda biyu. Shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi ta bayyana cewa 'yan majalisa 230 sun goyi bayan tsige shugaban yayin da 197 suka ki amincewa. Laifin Mista Trump na farko shi ne kokarin tursasa shugaban Ukraine da ya binciki abokin hamayyarsa, a zabe mai zuwa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden. Laifi na biyu kuwa ya hada da kokarin kawo wa majalisa tarnaki. Mista Trump a yanzu ya zamo shugaba na uku da aka taba tsigewa. A yanzu dai kallo zai koma ga majalisar dattawa da yan jam'iyyar Republican da shugaban ke da rinjaye domin yi masa shari'ah. Masana na ganin zai yi wuya su amince da wannan mataki na majalisar wakilai. Shi kuwa Shugaba Trump ya mayar da martini ne a wani gangami a Michigan, yana nuni da cewa ko a jikinsa: ''Ya ce na fada a wasikata da na aika wa Pelosi cewa, ci gaba d...

Naira dubu 700 ake biyana fansho - Tsohon gwamna

Image
Balarabe Musa Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ko alawus na musamman na daruruwan miliyoyin naira. Tsohon gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya ce N741,000 ake biyansa fansho a matsayinsa na tsohon gwamna. Ya ce tsoffin gwamnoni a jihar Kaduna, sun amince su karbi fansho daidai da wanda Famanan Sakatare na jiha ke karba. Al'amarin ya ja hankali ne bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya nemi gwamnatin jiharsa ta biya shi naira miliyan 10 a kowane wata a matsayin alawus na musamman, kamar yadda wata dokar jihar ta tanadar. Amma a ranar Talata ne majalisar dokokin jihar ta soke ta, tana mai cewa tsoffin gwamnonin jihar kafin shi sun shafe shekaru ba a biya su kudaden ba a zamanin mulkinsa na shekaru takwas. Wasu masana na ganin cewa bai kamata a ci gaba da biyan tsoffin gwamnoni irin wannan kudin ba, idan aka yi la'akari da matsain tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya. Masana irinsu Farfesa Jibr...

CISLAC ta yaba wa Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Image
Gwamna Bello Matawalle Kungiyar Nan mai fafutukar yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya, CISLAC ta ce matakin da gwamnan jihar Zamfara ya dauka na soke dokar da ta amince a bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakansu fansho abun a yaba ne. A wata sanarwa da shugaban kungiyar a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi koyi da jihar ta Zamfara wajen ganin an rage kashe kudaden gwamnati. Kungiyar ta kuma nemi sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da gwamnan na Zamfara. Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce zai yi amfani da fanshon tsoffin gwamnoni da ya soke wajen raya karkara. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin ya fitar, gwamna Matawalle ya yi takaicin yadda tsohon gwamna ya ke neman a biya shi makudan kudade a dai-dai lokacin da sauran 'yan fansho a jihar ke cikin kangin wahala saboda rashin biyan su kudadensu. Ya kara da cewa 'yan fansho na bin gwamnatin da ta shude bashin kudade da suka kai naira bilyan 10. Su...

Shirin yarjejeniyar zaman lafiya na Nan daram

Image
Gwamna Bello Matawalle Bayan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mutane da dama na nuna fargabar cewa yarjejeniyar sulhu da gwamnatin jihar ta kulla da 'yan bindgar domin su ajiye makamansu na neman wargajewa. A jiya ne dai aka kai hari garin kuma suka kashe mutane akalla goma sha takwas. Hukumomi dai sun bayyana cewa ga alama harin na ramuwar gayya ne bayan da 'yan sintiri da ake kira 'yan sa-kai suka kashe 'yan bindiga kimanin goma a farkon wannan wata. Mai bai wa gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan lamuran tsaro, Abubakar Muhammad Dauran, ya shaida wa manema labarai cewa yarjejeniyar ba ta wargaje ba tana nan tana aiki. Ya kuma ce gwamnati a shirye take ta ci gaba da karbar makaman, haka kuma ta bai wa shugabannin fulani umarnin karbe makamai daga hannun matasansu.  Jihar Zamfara dai ta yi fama da matsalolin tsaro sosai a shekarun da suka gab...